Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Kashe-kashe Ya Ci Gaba A Mangu Duk Da Dokar Ta-ɓaci A Yankin

Ana cigaba da kashe-kashe da ƙona gidaje a garin Mangu da ke ƙaramar hukumar Mangu ta Jihar Filato duk da dokar hana fita ta sa’o’i 24 da gw...



Ana cigaba da kashe-kashe da ƙona gidaje a garin Mangu da ke ƙaramar hukumar Mangu ta Jihar Filato duk da dokar hana fita ta sa’o’i 24 da gwamnati ta kafa.

Gwamna Celeb Mutfwang ne ya sanya dokar ta-ɓaci bayan da aka samu sabbin kashe-kashe a yankin, ranar Talata.

Sai dai an cigaba da tashin hankalin yayin da mazauna garin Mangu suka tabbatar da cewa ‘yan bindiga sun afkawa al’ummomi da dama, inda suka yi ta harbin kan mai uwa da wabi.

Rahotanni sun ce maharan sun ƙona gidaje da suka haɗa da makarantar Sunnah Islamiya da ke kan titin Gindiri.

Wani mazaunin Mangu mai suna Suleiman Muhammad ya shaida wa manema labarai cewa “da misalin ƙarfe 9:30 na safiyar yau 'yan bindiga ɗauke da manyan muggan makamai suka zo suka fara harbe-harbe kai tsaye.

“Sun kona gidaje da dama ciki har da makarantar Sunnah Islamiyya. An kashe wasu mutane. Sun mamaye jami'an tsaro a yanzu haka a garin Mangu, gaba ɗaya ‘yan bindigar sun kewaye mu.”

Kakakin rundunar ‘Operation Safe Haven’ mai wanzar da zaman lafiya a yankin, Captain Oya James, har yanzu bai amsa tambayoyin manema labarai ba.

No comments