Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Kwandon Shara Ne Ya Fashe Ba Bom Ba - ’Yan Sandan Abuja

Rundunar ’yan sandan babban birnin tarayya Abuja ta mayar da martani kan rahoton fashewar wani abu a unguwar Maitama da ke babban birnin. ...


Rundunar ’yan sandan babban birnin tarayya Abuja ta mayar da martani kan rahoton fashewar wani abu a unguwar Maitama da ke babban birnin.

A cikin shafin X a ranar Laraba, wasu mazauna yankin sun danganta lamarin da bam.

Sai dai rundunar 'yan sandan babban birnin tarayya Abuja, a cikin wata sanarwa da jami’ar hulɗa da jama’a ta rundunar ’yan sandan, SP Josephine Adeh ta fitar, ta ce lamarin ya faru ne sakamakon wani kwandon shara na ƙarfe da aka cika ya wuce kima, shi ne har ya yi bindiga.

“Rundunar ’yan sandan babban birnin tarayya Abuja na son sanar da jama’a game da fashewar wani abu da ake zargin ya faru a ranar 24/01/2024 da misalin ƙarfe 11 na safe kusa da wani juji a wajen harabar ofishin kasuwancin gwamnati da ke Maitama, Abuja.”

An tura tawagar masu ba da amsa cikin gaggawa da kuma mambobi na sashin kula da bama-bamai don tantance halin da ake ciki kuma binciken farko ya nuna cewa wani kwandon shara da aka cika kuma ala rufe da ƙarfe ne ya yi bindiga saboda tsanani zafin rana, wanda hakan ya yi sanadin raunata mutum biyu daga cikin masu aikin, waɗanda a halin yanzu ke samun kulawa a babban asibitin Maitama.

“Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja ta buƙaci jama’a da su yi taka-tsan-tsan tare da kaurace wa amfani da kwandon shara na ƙarfe. Maimakon haka, muna ba da shawarar yin amfani da kwantena na filastik ko roba don zubar da shara, saboda suna haifar da raguwar haɗarin al'amura da suka shafi kwantena masu zafi da ƙarfe mai zafi," inji sanarwar.

No comments