Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang ya sanya dokar hana fita ta awanni 24 a Ƙaramar Hukumar Mangu. Dokar za ta soma aiki nan take. Mataki...
Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang ya sanya dokar hana fita ta awanni 24 a Ƙaramar Hukumar Mangu. Dokar za ta soma aiki nan take.
Matakin na ƙunshe ne cikin wata sanarwar da Daraktan yaɗa labarai da harkokin al'umma na jihar, Gyang Bere ya sanya wa hannu.
Ya ce an ɗauki matakin ne saboda taɓarɓarewar harkokin tsaro a yankin.
Sanarwar ta ƙara da cewa "Gwamna Mutfwang ya ɗauki matakin ne bayan tuntuɓa da hukumomin tsaro."
Matsalar tsaro na cigaba da karuwa a jihar ta Filato. Ko a baya-bayan nan an kai wasu jerin hare-hare da suka yi sanadin mutuwar fiye da mutum 100 da jikkatar wasu da dama. An kuma kona wasu gidaje.
No comments