Daga Awwal Umar a Minna Kamar yadda manomi, Gwamna Umar Mohammed Bago na jihar Neja ya shelanta ƙudurin gwamnatin sa na dawo da martabar nom...
Daga Awwal Umar a Minna
Kamar yadda manomi, Gwamna Umar Mohammed Bago na jihar Neja ya shelanta ƙudurin gwamnatin sa na dawo da martabar noma don samar da guraben ayyuka ga jama'a, abu ne mai muhimmanci da kowane mai kishi da son ci gaban jiha ta yadda gwamnati za ta samu damar magance matsalolin rashin aikin yi da dogaro ga gwamnati da kuma samun kuɗaɗen shiga.
Kan haka ne, wakilin mu ya zanta da wasu masana kan shawarwarin da za su bai wa gwamnatin da kuma hanyoyin da gwamnatin za ta bi dan samun wannan nasarar.
Hon. Garba Ibrahim Nasalka, shi ne shugaban ƙungiyar masu fataucin kayan amfanin gona ta ƙasa, reshen jihar Neja. Ya ce wannan ƙuduri ne mai kyau idan an bi matakan da suka dace.
Ya ce, rahoton da aka samu na amfanin gonaa wannan shekarar, jihar Neja ta samu ƙarin mataki kan noman riɗi, inda a baya jihar ke samun kaso goma cikin ɗari na noman riɗi a ƙasar nan.
Ya ci gaba da bayyana cewa, a wannan shekarar, jihar Neja ta noma kaso arba'in da biyar cikin ɗari na noman riɗi, amma a bana, a yankin Arewa ta Kudu kawai, idan muka dubi ɓangaren waken soya, jihar ta samar da kaso talatiin da biyar cikin ɗari na wanken soyar da noma.
"Ka ga ke nan, idan gwamnati za ta ƙarfafa manoma kan noman shinkafa, masara da dawa, to ina da tabbacin jihar za ta iya zamowa ta ɗaya a ɓangaren noman amfanin gona saboda kyan yanayi da sauƙin noma da kuma yanayin ƙasar noman da ake iya nomawa sau uku a shekara.
"Ko bayan yalwar abinci, al'ummomi da dama za su samu ƙwarin gwiwar cewar gwamnatin da gaske take, kuma za a iya samun ƙarin hanyoyin samun kuɗaɗen shiga saboda kwararowar 'yan kasuwa masu safarar kayan abinci."
A ƙarshe ya Hon. ya ce, "Shawarar da zan bai wa gwamnati, shi ne inganta tsaro, horar da manoma da ba su shawarwarin da ya dace. Idan aka bi watannan hanyoyin, tabbas za a cimma gaci.
Shi kuwa Malam Lawal Yaro, wani mai harkar saye da sayar da filaye, cewa ya yi, maganar noma a jihar nan, abu ne da dole gwamnati ta bada na ta gudunmawa wajen hana ƙananan manoma sayar da filayen noma.
Ya ce, "Yanzu idan ka dubi ɓangaren Neja ta Tsakiya, inda manoman ta suka yi ƙaurin suna wajen noman doya, kashi tamanin cikin ɗari na filayen noma sun ƙare, domin an sayar wa masu hannu da shun, kuma da yawan su bayan sun saye ƙasar noman, sun killace su ba su noma ba, kuma ba su bai wa manoman damar nomawa ba.
sannan ba kyakkyawar yanayin tsaron da zai bai wa manoman damar kutsawa cikin dazuka dan ci gaba da aikin noman, saboda barazanar 'yan bindiga, na hana manoman damar zuwa gonakin su na kulawa ko girbe amfanin gonar.
"Tilas ta sanya wasu manoman yin hijira daga matsugunnan su na asali zuwa wasu yankuna ko barin jihar ma baki ɗaya.
"Ya kamata a samar da ƙudurin dokar da za ta hana sayar da filayen gonar da ta kai hekta biyar zuwa sama, domin za ka iske iyalin da ke noma hekta biyar zuwa sama wanda shi ne abin da iyalin suka mallaka ta hanyar gado ko saye da suke cin anfanin sa sun ɗaiɗaice, ka ga dole a samu kwararar jama'a daga cikin karkara zuwa birane dan neman abinci, sannan ga ayyukan yi sun ƙaranci a cikin karkara.
No comments