'Yan bindiga sun sako 'yan matan nan biyar daga cikin shida da suka sace a yankin Bwari da ke Abuja, Babban Birnin Tarayya. Hakan ...
'Yan bindiga sun sako 'yan matan nan biyar daga cikin shida da suka sace a yankin Bwari da ke Abuja, Babban Birnin Tarayya.
Hakan ya biyo bayan kashe ɗaya daga cikin ’yan matan mai suna Nabeeha kimanin mako biyu da suka gabata.
Kisan Nabeeha abu ne da ya tayar da hankalin al’ummar Nijeriya, musamman tun bayan da matsalar garkuwa da mutane ta fara tsananta a yankin Abuja.
'Yan uwan Nabeeha sun tabbatar da komawar 'yan matan biyar gida a cikin daren Asabar.
Haka zalika hotunan bidiyon komawar 'yan uwan Nabeeha na ta yawo a shafukan sada zumunta, inda 'yan ƙasar ke ta san barka da farin cikin sakin matan.
No comments