Wani mummunan haɗarin mota ya yi sanadin mutuwar mutum 16 tare da jikkata huɗu a Tashar Yari da ke kan babban titin Kaduna zuwa Kano. Babban...
Wani mummunan haɗarin mota ya yi sanadin mutuwar mutum 16 tare da jikkata huɗu a Tashar Yari da ke kan babban titin Kaduna zuwa Kano.
Babban kwamandan Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa mai lura da shiyyar Kaduna, Kabir Y Nadabo ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.
Ya ce haɗarin, wanda ya rutsa da motar bas ɗauke da fasinjoji aƙalla 20, ya faru ne da misalin ƙarfe 11:20 na safiyar ranar Lahadin.
Kabir Y Nadabo ya ce gudun wuce-kima ne ya haifar da mummunan hatsarin, inda motar ta faɗa cikin rami.
Babban kwamandan ya ce tuni aka kai mutum huɗun da suka jikkata zuwa babban asibiti Maƙarfi, domin ba su kulawar gaggawa, yayin da aka kai gawarwakin waɗanda suka mutu zuwa asibitin koyarwa na Shika da ke Zariya.
No comments