Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Masu Garkuwar Da Suka Sace Mutune A Rukunin Gidajen Sojojin Abuja, Sun Bukaci Miliyan N30

Masu garkuwa da mutane da suka sace wata matar Barista Cyril Adikwu da surukan sa biyu daga rukunin gidajen Army Estate da ke Kurudu, Abuja,...

Masu garkuwa da mutane da suka sace wata matar Barista Cyril Adikwu da surukan sa biyu daga rukunin gidajen Army Estate da ke Kurudu, Abuja, sun nemi kuÉ—in fansa sama da Naira Miliyan 30.

Idan za a iya tunawa, masu garkuwa da mutanen sun kai farmaki gidan ne a daren Alhamis da misalin ƙarfe 10:00 na dare, suka tafi da matarsa da surukansa biyu.

Da yake zantawa da jaridar Vanguard game da lamarin, Barista Cyril Adikwu wanda ya tsere yayin da masu garkuwa da mutanen suka zo gidan sa da ke yankin, ya ce yana tattaunawa da masu garkuwar, kuma sun buƙaci a biya su kuɗin fansa sama da naira miliyan 30 cikin ƙanƙanin lokaci.

Da yake magana da jaridar Vanguard, É—aya daga cikin jami’an kula da kadarorin da bai so a ambaci sunan sa ba ya ce hukumar tare da hadin gwiwar jami’an tsaro suna kokarin kuÉ“utar da waÉ—anda aka yi garkuwa da su.

No comments