Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya ce jami'an tsaro sun kama wasu mutane da ake zargi da bai wa masu garkuwa da mutan...
Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya ce jami'an tsaro sun kama wasu mutane da ake zargi da bai wa masu garkuwa da mutane bayanan sirri a birnin Abuja.
Ministan ya bayyana hakan ne a lokacin wani babban taro da ya yi da shugabannin ƙananan hukumomi da sarakunan gargajiya da jami'an tsaro da mazauna yankin Gwagwalada a birnin.
Duk da cewa ministan bai bayyana adadin mutanen da aka kaman ba, ya buƙaci mazauna yankin Gwagwalada su kwantar da hankalinsu, saboda a cewar za a samu cigaba a yanayin tsaron birnin cikin kwanaki masu zuwa.
Mista Wike ya kuma umarci kwamishinan 'yan sandan birnin ya gaggauta samar da ƙarin ofisoshin 'yan sanda har guda biyu a Ƙaramar Hukumar Gwagwaladan.
Abuja dai a baya-bayan nan na cigaba da fuskantar matsalar tsaro musamman a makonnin baya-bayan nan inda masu garkuwa da mutane ke cigaba da sace mutane domin neman kuÉ—in fansa.
Masana harkokin tsaro da tattara bayanai sun ce an sace mutum 63 a birnin tarayyar Abuja daga ranar 1 gawatan Janairu zuwa 18 ga watan.
No comments