Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya bayyana cewa gwamnatin sa ba za ta amince da duk wani nau'i na cin hanci da rashawa ko rashin tau...
A ranar Alhamis ne gwamnan ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa na musamman a zauren majalisar a gidan gwamnati da ke Gusau.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta ce majalisar ta kasance taron zartarwa na farko na gwamnatin Zamfara a shekarar 2024.
Ya ƙara da cewa, Gwamna Dauda Lawal ya buƙaci dukkan masu riƙe da manyan muƙamai da kwamishinoni da masu ba da shawara na musamman da su fahimci manufar sa tare da saita ayyukan su.
Sanarwar gwamnan ta ce: Zuwa ga Kwamishinoninmu, Shugabannin Hukumomi da Ma'aikatunmu, ku ne Manyan Jami'an Gudanarwa a cikin gwamnati. An naÉ—a ku don samar da jagoranci na gari ne, ba don bayar da kwangila ko raba kayan aiki don cigaban kan ku ba.
“Ku ba ’yan kwangila ba ne; ku masu hidimta wa mutane ne. Dole ne ku cire tunanin cewa an naÉ—a ku don yin wani abu ban da hidima da inganta rayuwa É—imbin jama'a ta hanyar samar da kayan aiki da ababen more rayuwa da za su tallafa wa rayuwarsu da ayyukansu ba.
“Dole ne mu kawo canjin da ake buÆ™ata domin ciyar da jihar gaba; dole ne mu yi abubuwa iri daban.
“Ba mutanen jihar nan sun zaÉ“e mu ne don kawai mu maye gurbin fuskoki da halayen waÉ—anda suka gabace mu ba. An zaÉ“e mu ne don mu canja yadda ake gudanar da harkokin gwamnati.”
“Game da haka, ina gaya muku wannan a yau: Ba zan yarda da duk wani aiki na cin hanci da rashawa da rashin tausayi daga kowane mai riÆ™e da muÆ™ami ko ma’aikacin gwamnati ba. Na sha cewa ban zo nan don neman kuÉ—i ba, kuma duk wanda ke da burin arzuta kansa gara ya canja shawara ko kuma ya yi murabus daga gwamnati cikin mutunci.
No comments