Wasu ’Yan bindiga sun yi garkuwa da wasu mutum uku a rukunin gidajen da ke bayan gidajen tsoffin sojojin ƙasar da ke rukunin gidaje na Kurud...
Wasu ’Yan bindiga sun yi garkuwa da wasu mutum uku a rukunin gidajen da ke bayan gidajen tsoffin sojojin ƙasar da ke rukunin gidaje na Kurudu a babban birnin tarayyar Abuja.
Rahotonni daga ƙasar sun ambato daraktan hulɗa da jama'a na rundunar sojin ƙasar, Birgediya Onyema Nwachukwu na tabbatar da faruwar lamarin.
Birgediya Janar Nwachukwu ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:00 na daren ranar Alhamis.
Mazauna rukunin gidajen sun ce maharan sun buɗe wuta a rukunin gidajen kafin daga bisani su arce da mutanen da suka yi garkuwar da su.
Cikin wata hira da ya yi da gidan talbijin na Channels a ƙasar, Birgediya Janar Nwachukwu ya ce dakarun soji sun garzaya rukunin gidajen a lokacin da suka samu kiran gaggawa dangane da abin da ke faruwa.
Ya ƙara da cewa jami'ansu na ci gaba da farautar maharan domin kuɓutar da mutanen.
Unguwar Kurudu na ɗaya daga cikin garuruwan da ke kan iyakar Abuja da jihar Nasarawa.
No comments