Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Kotun Ƙoli Ta Tabbatar Da Nasarar Uba Sani, Inuwa Yahaya Da Aminu Bande

Kotun Ƙolin Nijeriya ta yi fatali da ƙarar da ɗan takarar jam'iyyar PDP a gwamnan Kaduna, Isah Ashiru wadda ke ƙalubalantar nasarar gwam...



Kotun Ƙolin Nijeriya ta yi fatali da ƙarar da ɗan takarar jam'iyyar PDP a gwamnan Kaduna, Isah Ashiru wadda ke ƙalubalantar nasarar gwamna Uba Sani.

Kotun ta kuma tabbatar da hukuncin da ƙananan kotuna suka yanke da ya tabbatar da nasarar Uba a zaɓen watan Maris din 2023.

A ranar 24 ga watan Nuwamba ne kotun ɗaukaka ƙara a Abuja ta tabbatar da nasarar gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna.

Sai dai kotun sauraron ƙararrakin zaɓe a nata ɓangaren ta samu rarrabuwar kai game da cancantar karar.

A ɗaya bangaren kuma, Kotun Ƙoli ta tabbatar da nasarar Inuwa Yahaya na Jam'iyyar APC a matsayin gwamnan jihar Gombe.

A ranar Juma’a ne kotun kolin ta yi watsi da karar da ɗan takarar jam’iyyar PDP, Jibrin Barde ya shigar na kalubalantar zaben gwamna Yahaya.

A hukuncin bai-daya da kwamitin alkalai ya yanke, kotun kolin ta ce karar ba ta da inganci.

Kazalika a zaman nata na yau, Kotun koli ta kori ƙarar da ɗan takarar jam'iyyar PDP Aminu Bande ya daukaka domin ƙalubalantar nasarar gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi.

Kwamitin alƙalan ya ce ƙarar ba ta cancanta ba.

No comments