HUKUMAR Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa (FRSC) ta tabbatar da mutuwar mutum 10, yayin da wasu 12 suka samu raunuka a wani hatsarin mota da ya rutsa d...
Kakakin hukumar, Ibrahim Yahaya ne ya tabbatar wa Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya (NAN) faruwar lamarin a Dutse.
Yahaya ya ce, hatsarin ya faru ne tsakanin wata mota ƙirar Volkswagen Golf da wata bas ƙirar Toyota Hiese a ƙauyen Gidan Garke da misalin ƙarfe 12:30 na ranar Alhamis.
Ya bayyana cewa hatsarin ya afku ne lokacin da motocin biyu ke ɗauke da fasinjoji 22, suka yi karo da juna sakamakon gudun wuce kima.
Kakakin ya ce jami’an hukumar sun kai waɗanda abin ya shafa zuwa babban Asibitin Ringim.
A cewarsa, jami’an ba su iya tantance lambobin motocin biyu ba saboda sun ƙone ƙurmus.
No comments