Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Shaikh Abduljabbar: Iyalan Malam Nasiru Kabara Sun Yi Addu'a Ta Musamman

  Da Yammacin wannan rana ne babban ɗan Shaikh Nasiru Kabara, wato Shaikh Ibrahim Mua'azzamu da kuma ƙannin sa, haɗi da Almajiran Shaikh...

 

Da Yammacin wannan rana ne babban ɗan Shaikh Nasiru Kabara, wato Shaikh Ibrahim Mua'azzamu da kuma ƙannin sa, haɗi da Almajiran Shaikh Nasir Kabaran suka gabatar da addu'a ta musamman game da halin da ɗan uwan su, Shaikh Abduljabbar Nasiru Kabara yake ciki a halin yanzu.

Taron addu'ar, wanda aka yi daidai da munasabar cika shekaru shida da rasuwar Shaikh Aliyul Kwawwasu, wanda iyalan suka jima da nuna zargin musabbabin mutuwar sa, da cewar guba aka ba shi. 

A wurin wannan addu'a ta musamman, an yi saukan karatun Alƙur'ani mai tsarki, tare da wasu addu'o'i ga mamacin da kuma nema wa Malam Abduljabbar mafita a wurin Allah. 

Haka kuma Iyalan na Shaikh Nasiru Kabara sun sake jawo hankalin gwamnatin tarayya da ta jihar Kano, kan cewa abin da aka ce Shaikh Abduljabbar ya faɗa, sharri da juya zance ne aka yi masa

Shaikh Sidi Musal Ƙasuyuni Nasiru Kabara da sauran mahalarta taron, sun yi addu'ar neman jaddada rahamar Allah ga ruhin mamacin, watoo Shahid Aliyul Kwawwasu, tare da fatan Allah dafa wa Shaikh Abduljabbar bisa halin da ya ke ciki.

No comments