Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamna Lawal Ya Tallafa Wa Tsofaffin Sojojin Zamfara Da Naira Miliyan Biyar, A Ranar Tunawa Da Su

  Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya ƙaddamar da Tambarin Ranar Tunawa da Sojoji ta Shekarar 2024, inda ya yi alƙawarin tallafa wa iyala...


 

Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya ƙaddamar da Tambarin Ranar Tunawa da Sojoji ta Shekarar 2024, inda ya yi alƙawarin tallafa wa iyalan sojojin da Naira Miliyan Biyar.

A wajen ƙaddamar da taron a ranar Juma’a, Gwamna Lawal ya samu kyautar tambarin daga shugaban tsofaffin sojoji na Nijeriya reshen jihar, Alhaji Aminu Ladan Mada, a gidan gwamnati da ke Gusau.

A wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta ce gwamnatin jihar ta tallafa wa reshen jihar Zamfara da kuɗin Naira Miliyan 5.

Ya ƙara da cewa, gwamnatin jihar Zamfara ta duƙufa wajen bayar da tallafi, wanda ke da matuƙar muhimmanci, musamman ganin yadda ranar tunawa da sojojin ƙasar ke da muhimmanci.

Ya ce, “Yayin da yake ƙaddamar da tambarin tunawa da sojojin ƙasar nan na shekarar 2024 a Gusau, Gwamna Lawal ya gabatar da ƙudurinsa na goyon bayan rundunar sojojin Nijeriya, tare da nuna jin daɗin sa kan sadaukarwar da jarumai suka yi.

A jawabin da ya gabatar, Gwamnan ya bayyana wasu daga cikin goyon bayan da gwamnatin sa ke bai wa rundunar sojojin Nijeriya reshen jihar, da suka haɗa da ɗaukar tsofaffin sojojin sama da 50 cikin jami’an Runduna ta musamman don kare jama’a, wanda jihar ke shirin ƙaddamarwa.

“Dole ne mu yaba da gudumawar da jajirtattun sojojin mu suke bayarwa wajen yaƙi da ‘yan fashi, ta’addanci, da sauran nau’ukan laifuka a faɗin ƙasar nan.

“Haƙƙi ne na haɗin gwiwa don tabbatar da ingantacciyar walwala ga Sojojin Nijeriya da iyalan Jaruman da suka mutu, waɗanda suka sadaukar da rayuwarsu domin wanzar da zaman lafiya.

“Bugu da ƙari kuma, mun sanya mambobi 50 na rundunar sojojin Nijeriya domin shiga cikin ƙungiyar kare haƙƙin jama’a, ɓangaren tsaro da ke tallafa wa sojoji wajen kare jiharmu.”

No comments