Daga Musa Muhammad Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa ta Tarayya, Sanata Barau I. Jibrin ya tallafa wa al'ummar jihar Kano da motoci...
Daga Musa Muhammad
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa ta Tarayya, Sanata Barau I. Jibrin ya tallafa wa al'ummar jihar Kano da motoci guda Sittin, ƙirar Sharon. Wannan na cikin ƙudurin Sanatan na tallafa wa al'ummar Kanon da kewaye.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Sanatan, Alhaji Ismail Mudashir ya sanya wa hannu, ya bayyana cewa dubban mutane ne daga Mazabu, magoya baya da masu fatan alhairi suka shaidi wannan rabon, wanda ya gudana a harabar "Meena Events Centre da ke Kano.
Alhaji Mudashir ya kuma bayyana cewa mutane ne daga fannoni daban-daban suka amfana da wannan tallafi na Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan, waɗanda suka haɗa da 'yan kasuwa manoma, ma'aikatan gwamnati, 'yan siyasa da sauran su.
Kamar yadda wakilin sa a wurin taron, kuma Shugaban ma'aikatan ofishin sa, Farfesa Muhammad Ibn Abdullahi ya bayyana, Sanata Barau ya raba waɗannan motoci ne don ya sauƙaƙa wa waɗanda suka amfana, don zuwa wuraren harkokin su, tare da inganta tattalin arzikin jihar.
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan, ya kuma bayyana irin jajircewar sa wajen ganin al'ummar Mazaɓar sa sun samu abubuwan dogaro da kai, tare da inganta tattalin arzikin ƙasar nan..
Daga nan ya hori waɗanda suka amfana da wannan tagomashi, su tabbatar sun amfani da motocin, musamman wajen sauya rayuwar su da ta sauran al'ummar yankin.
“Wannan aiki, ba shi be na farko ba, kuma ba shi ne na ƙarshe ba, in Allah ya yarda. Za mu ci gaba da aiwatar da shirye-shiryen mu na kyautata rayuwar jama'a don su zama masu dogaro da kan su," ya ce
No comments