Gwamnan Jihar Kaduna Sanata Uba Sani, ya tabbatar da harin da ’yan bindiga suka kai wasu ƙauyuka uku a Ƙaramar Hukumar Kaura, inda suka kash...
Sai dai rundunar ’yan sandan jihar ta musanta cewa an kai harin a Kudancin Kaduna.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Mansir Hassan, ya ce rundunar ta yi tuntuɓa da dama a cikin yankuna da abin ya shafa amma babu tabbacin faruwar lamarin.
"Ba gaskiya ba ne, babu wani abu makamancin haka saboda mun tuntuɓi al'ummomin da abin ya shafa, babu wani abu makamancin haka," inji shi.
Hakan dai na zuwa ne kamar yadda wata majiya ta shaida wa wakilinmu cewa aƙalla mutane bakwai ne aka kashe yayin da ake fargabar an yi garkuwa da 54 a wani samame da wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton ‘yan fashi ne suka kai na tsawon sa’o’i a daren Laraba a unguwar Dawaki da ke ƙaramar hukumar Kauru ta jihar.
Ƙauyukan uku da aka ce rikicin ya shafa sun haɗa da Ungwan Sako, Kunkurai, da Dokan Kaji.
Aƙalla, 34 daga cikin mutanen yankin har yanzu suna cikin kogon ‘yan fashin yayin da aka ce mutanen yankin sun ceto 20 daga cikin waɗanda aka yi garkuwa da su.
Wata majiya ta ce, “’yan bindigar sun mamaye waɗannan yankuna ne sannan sula afka masu.
“’Yan bindigar kullum suna fitowa ne daga sassan Kajuru da dajin Kachia inda sansaninsu yake. Sansanin yana Dutsen Magunguna a ƙaramar hukumar Kajuru.
"Idan har sojoji ba su kai farmaki kan sansanonin su da ke kewayen yankunan ba, ba za a taɓa samun zaman lafiya ba."
A halin da ake ciki, gwamnan ya ce gwamnatin jihar ta samu labarin cewa ‘yan bindiga sun kai hari a yankin Dokan Karji na ƙaramar hukumar Kauru da wasu wurare a yankin Gefe na ƙaramar hukumar Kajuru.
A cewar gwamnan a shafin sa na Facebook da aka tabbatar a ranar Juma’a, a wadannan wurare an yi asarar rayuka, an yi garkuwa da wasu ‘yan yankin, wasu kuma sun jikkata.
Ya ƙara da cewa, hukumomi za su yi duk mai yiwuwa wajen ganin sun farauto masu aikata laifukan tare da gurfanar da su a gaban kuliya.
Gwamnan ya ce, “Mun samu labari daga jami’an tsaro cewa wasu ‘yan bindiga sun kai hari a yankin Dokan Karji na ƙaramar hukumar Kauru da wasu wurare a yankin Gefe na ƙaramar hukumar Kajuru.
“A wadannan wurare, an yi asarar rayuka, an yi garkuwa da wasu ‘yan yankin, wasu kuma sun jikkata a hare-haren marasa daɗi.
“Muna yin Allah wadai da waɗannan ayyukan ta’addanci. Masu aikata wadannan munanan laifuka ba su da gurbi a cikin al’umma mai wayewa irin tamu ba. Za mu bi duk wata hanya don farauto su, mu gurfanar da su a gaban kotu.
Ya ƙara da cewa “Ma’aikatar tsaron cikin gida da harkokin cikin gida ta na aiki tare da jami’an tsaro wajen daƙile waɗannan miyagun da suka bar baya da ƙura na zubar da jini da hawaye da raɗaɗi.
No comments