* Ya yi alƙawarin inganta harkokin kiwon lafiyar al'ummar Zamfara Gwamna Dauda Lawal ya yi alƙawarin inganta harkokin kiwon lafiya a Jih...
* Ya yi alƙawarin inganta harkokin kiwon lafiyar al'ummar Zamfara
Gwamna Dauda Lawal ya yi alƙawarin inganta harkokin kiwon lafiya a Jihar Zamfara.
A ranar Asabar ɗin da ta gabata ne gwamnan ya aza harsashin gini, a ƙoƙarin gyara babban asibitin Ƙaramar Hukumar Anka.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ta ce, za a gyara babban asibitin garin Anka ne domin inganta harkokin kiwon lafiya ga jama’a.
Ya ƙara da cewa, gwamnan ya je ƙaramar hukumar watannin da suka gabata, inda ya duba babban asibitin Anka sannan ya gano wuraren da ke buƙatar a inganta su.
Ya ce, “A yau ne Gwamna Dauda Lawal ya ƙaddamar da aikin gyara babban asibitin Anka a wani nangare na ƙudirin gwamnatinsa na ganin an samar ingantaccen kiwon lafiya a jihar.
“Gwamnatin jihar za ta gyara tare da samar da cikakken kayan aiki ga manyan asibitocin da ke dukkanin ƙananan hukumomin jihar Zamfara.
A nasa jawabin, Gwamna Lawal ya sake jaddada cewa ya yi alƙawarin gyara babban asibitin Anka, kuma ga shi a yau ya cika alƙawarin sa.
“Kamar yadda Daraktan Likitoci na Asibitin ya shaida, an tanadi isassun kuɗaɗen gyara da kayan aiki. Za a kammala aikin ba tare da wani shamaki ba, In Sha Allah.
“Muna samun ci gaba a yaƙi da rashin tsaro kuma za mu cigaba da lalubo sabbin hanyoyin inganta rayuwar al’ummarmu. Wannan shi ne farko.
No comments