Daga Abdullahi Muhammad Sheka Lokacin da al'ummar Nijeriya ke dakon Hukuncin kotun ƙoli da ya shafi ɗan takarar kujerar Gwamnan Kano da...
Daga Abdullahi Muhammad Sheka
Lokacin da al'ummar Nijeriya ke dakon Hukuncin kotun ƙoli da ya shafi ɗan takarar kujerar Gwamnan Kano da Mataimakinsa, babban Daraktan haɗaɗɗiyar ƙungiyar masu goyon bayan Jam'iyyar APC na ƙasa, Injiniya Kailani Muhammad ya shiga tsare-tsaren haɗa Kan masu goyon Jam'iyyar na Jihohin Arewa Maso Yammacin ƙasar nan bisa kyakkyawan fatan da ake yi na samun Nasarar Jam'iyyar ta APC.
Injiniya Kailani Muhammad yana da yaƙinin cewa, "Bisa kyakkyawan zaton da muke wa kotun ƙoli, munna fata, Addu'a tare da tabbacin da muke da shi na cewa, Shari'ar da ke gaban kotun ƙolin za ta ta bai wa ɗan takarar mu na Gwamna da Mataimakin sa, Dakta Nasiru Yusif Gawuna da Alhaji Murtala Sule Garo Nasara."
Daraktan yaɗa labaran Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Abba Anwar ne ya Shaida wa manema labarai a Kano cikin makon nan.
Ya ce, hakazalika Kailani ya jinjina wa Shugaban Jam'iyyar APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje CON, bisa kasancewa guda cikin masu kyakkyawan tsara tafiyar APC wajen samun nasar.
Babban Daraktan ya Kuma aminta da cewa, Gawuna da Garo za su zama masu cikakkiyar biyayya ga Shugaban Jam'iyyar APC, Jam'iyya da kuma Dimokraɗiyyar baki ɗaya.
"Sakamakon addu'o'in da muke yi da kyakkyawar niyya, muna da tabbacin Jam'iyyar APC za ta samu nasara a kotun ƙoli. Hakan ta sa nake cewa, a madadin ɗaukacin mambobin haɗakar pungiyoyin da suke goyon bayan Jam'iyyar APC, cewa yanzu haka mun fara gangamin shiyyar Arewa Maso Yamma na Jihohi 7 domin bikin murna, tare da nuna goyon bayan mu ga Gwamnati mai shigowa ta Gawuna da Garo " In ji shi.
Ya ƙara da cewa, Kano za ta karɓi baƙuncin dubban ɗaruruwan magoya baya, wanda ba a taɓa ganin irinsa ba a tarihin siyasar Jihar Kano.
Ya Kuma tabbatar da cewa Gwamnatin Gawuna da Garo za ta zama kamar Gwamnatin Ganduje ta fuskar ingantaccen tsaro, girmama Sarakuna, tallafa wa matasa maza da Mata, ci gaban tattalin arziki, Inganta harkar ci gaban al'umma da sauran su."
Injiniya Muhammad ya ƙarƙare jawabin nasa da jinjinar su ga irin salon mulkin Ganduje wajen mulkar Jam'iyyar APC a Matsayin Shugaban jam'iyyar na Ƙasa, inda ba kawai samar da daidaito kaɗai ba, har ma da nagartaccen jagorancin Jam'iyyar da harkokin gudanarwa, siyasar Jam'iyya da Dimokraɗiyyar baki ɗaya
No comments