Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamna Lawal Ya Ƙaddamar Da Wasu Manyan Ayyuka A Ƙauran Namoda

  -Waɗanda Suka Haɗa Da Cibiyar Koyar Da Sana'o'i, Makarantun Tsangaya, Cibiyar Inganta Harkokin Mata Da Babban Asibiti Jiya Alhamis...


 

-Waɗanda Suka Haɗa Da Cibiyar Koyar Da Sana'o'i, Makarantun Tsangaya, Cibiyar Inganta Harkokin Mata Da Babban Asibiti

Jiya Alhamis ne Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya ziyarci Ƙaramar Hukumar Ƙauran Namoda, inda ya ƙaddamar da wasu ayyukan ci gaban al'umma. Gwamnan ya jaddada cewa yanzu Zamfara na gab da zama sabuwa. 

Wannan ziyarar aiki ta Gwamnan ya kai a Ƙaramar Hukumar Ƙauran Namoda, ta zo ne kwana ɗaya bayan da ya ƙaddamar da rabon Injinan noma da kayan amfanin gona a yankin Zamfara ta Arewa, a Ƙaramar Hukumar Shinkafi. 

Sulaiman Bala Idris, shi ne mai magana da yawun Gwamnan, inda a cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu, ya bayyana cewa, waɗannan ayyuka da Gwamnan ya ƙaddamar, suna da matuƙar muhimmanci a shirin su na ceto jihar Zamfara. 

Ya ce, za a gina cibiyoyin horar ta matasa uku-uku a kowace ɗaya daga cikin mazaɓun Sanata uku da ke jihar. Za a gina waɗannan cibiyoyi a Ƙaramar Hukumar Gusau, ta yankin Zamfara ta Tsakiya. Ƙaramar Hukumar Ƙauran Namoda, ta yankin Zamfara ta Arewa, sai kuma Ƙaramar Hukumar Gummi, ta yankin Zamfara ta Yamma.

Ya ce, “Jiya, Gwamna Dauda Lawal ya ɗauki wani ƙwaƙƙwaran mataki na ganin ya cika alƙawuran da ya ɗauka a lokacin yaƙin neman zaɓe, inda ya ƙaddamar da wasu muhimman ayyukan raya ƙasa a Ƙaramar Hukumar Ƙauran Namoda.

“Gwamnan ya ƙaddamar da ginin Cibiyar koyar da sana'o'in hannu da Cibiyar horar da matasa a Kwalejin ƙere-ƙere ta gwamnati da ke garin Kauran Namoda. Cibiyar, tana da ajujuwa shida, ɗakin gwaje-gwaje, ɗakunan koyar da ayyukan hannu, ɗakin Kwamfutoci da kuma ofisoshin Malamai. 

“A lokacin ƙaddamarwar, Gwamna Lawal ya jaddada cewa ilimi na ɗaya daga cikin abubuwa muhimmai da gwamnatin sa ta sanya a gaba, kuma masu ruwa da tsaki na nan suna haɗa ƙarfi da ƙarfe don ganin an cimmar nasarar yi wa harkar ilimi garambawul a jihar."

Sauran ayyukan da Gwamnan ya ƙaddamar a wannan Ƙaramar Hukuma, sun haɗa da gina Cibiyar inganta harkokin mata, makarantun Tsangaya da sake gina babban asibitin gwamnati da ke Kauran Namoda.

“Cibiyar inganta harkokin mata, za ta kasance wuri ne na tallafa wa mata. Cibiyar, za ta ƙunshi duk wasu kayan horarwa na zani isassu. 

“A wurin ɗora tubalin sake ginin babban asibitin gwamnati na Kauran Namoda, Gwamna Dauda Lawal ya yi alwashin samar da ƙwararrun Likitoci da Nas-nas, tare da ƙara jaddada aniyar sa ta wadata jihar da isassun kayan kula da lafiya. 

“A wajen ƙaddar da makarantu Islamiyya na Tsangaya kuwa, Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatin sa za ta gina irin wannan makaranta a duk yankuna uku na jihar. Wannan wani shiri ne da aka yi da nufin zamanantar da makarantun Tsangaya, da kuma samar da wasu damarmaki ga ɗalibai."

No comments