A yau Alhamis ne Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya dira Ƙaramar Hukumar Shinkafi, inda ya raba wa manoma Injinan noma da sauran kayan...
A yau Alhamis ne Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya dira Ƙaramar Hukumar Shinkafi, inda ya raba wa manoma Injinan noma da sauran kayan fanin gona, wanda ya gudana a Gidan Noma da ke Ƙaramar Hukumar ta Shinkafi.
Wannan tagomashi da Gwamnan ya yi wa Zamfarawan, ya yi shi ne yankin Arewacin jihar a ƙarƙashin shirin nan na sauƙaƙa wa jama'a daga Korona na 'Coronavirus (COVID-19) Action Recovery and Economic Stimulus (N-CARES)'.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya sanya wa hannu, ya bayyana cewa za a ƙaddamar da irin wannan rabon a duk yankunan Mazaɓun jihar guda uku.
Ya ce, an fara ƙaddamar da wannan shiri ne a yankin Zamfara ta Tsakiya a ranar Laraba da ta gabata a Gusau.
Sanarwar ta ce, “Yau Gwamna Dauda Lawal ya ƙaddamar da rabon injinan noma da kayan amfanin gona, inda jama'ar yankin Zamfara ta Arewa suka amfana.
“Waɗanda suka amfana, sun samu duk wani abu da ake buƙata a harkar noma, kamar su iri da sauran su na shekara huɗu.
“Gwamnatin jihar Zamfara ta duƙufa wajen dumfarar harkar noma, musamman wajen samar da Injinan noma da sauran abubuwan more rayuwa da yankunan karkara suka fi buƙata.
"Wannan tallafi zai bayar da gagarumar gudumawa wajen ganin jama'ar da ke yankunan karkara sun samu nasara wajen inganta harkar noman su don kyautata rayuwar jama'ar su."
Sanarwar ta ce, cikin jawabin Gwamna Lawal a wurin taron, ya bayyana cewa gwamnatin sa ta yanke shawarar samar da hanyoyin da manoma za su daina asarar kayan amfanin gonar su.
Gwamnan ya ce, “Da taimakon Allah Maɗaukakin Sarki, mun mayar da hankali a kashi na biyu na shirin noman FADAMA III, da niyyar ingantawa, tare da ƙarfafa hanyoyin samar da wadataccen abinci.
“Ganin hanyoyi da sauran abubuwan inganta rayuwa a yankunan karkara, suna da matuƙar muhimmanci wajen samar da amfanin gona, gwamnati na ta shirya gina hanyoyi masu kilomita 70, da gina sabbin kasuwanni 40, waɗanda za su ƙunshi shaguna 4,000.
"Wannan zai dawo mana da harkokin tattalin arzikin mu, wanda aikin ta'addanci ya gurgunta, kuma zai zama hanyar samar da tsaftatattun kayan amfanin gona.
No comments