Hukumar kula da jin daɗin Alhazai ta jihar Kaduna ta yaba wa Hukumar ta ƙasa NAHCON, bisa ƙarin wa'adin da ta yi na karɓar kuɗin aikin H...
Hukumar kula da jin daɗin Alhazai ta jihar Kaduna ta yaba wa Hukumar ta ƙasa NAHCON, bisa ƙarin wa'adin da ta yi na karɓar kuɗin aikin Hajjin bana na 2024, inda ta yi kira ga maniyyatan Jihar da kar su sake da wannan dama da aka samu.
Cikin wata sanarwa da Kakakin Hukumar, Yunusa Mohammed Abdullahi ya sanya wa hannu, ya ambato shugaban Hukumar, Malam Salihu S. Abubakar yana cewa, wannan ƙarin lokaci zuwa 31 ga watan nan na Janairu ya zo ne sakamakon kiraye-kirayen da Malamai da sauran masu ruwa da tsaki a harkar aikin Hajjin suke ta yi na a ƙara wa'adin.
Saboda haka ne Shugaban Hukumar, Malam Salihu ya yi kira ga maniyyatan kan cewa su yi amfani da wannan dama su cikasa kuɗin da suka ajiye kafin ranar da aka sake sanyawa.
"Wannan ya samar da wata dama ga waɗanda ba su yi rajista ba, su hanzarta don samun shiga cikin matafiyan na bana," in ji Malam Salihu.
Daga nan shugaban ya tunatar da maniyyatan cewa ana yin rajistar maniyyatan ne kawai ta hannun wakilan Hukumar da ke a Ƙananan Hukumomin jihar 23.
A nan ne Malam Salihu ya bayyana wa Maniyyatan cewa ana fara yin rajistar ne daga karɓar takardar banki ta hannu waɗancan jami'an da ke Ƙananan Hukumomin da aka ambata.
Ya ce, Hukumar a shirye ta ke wajen samar da duk abubuwan da suka wajaba don gudanar da aikin Hajji mai cike da nasara. Inda kuma ya yi kira ga maniyyatan su dage wajen hanzartawa don amfani da wanan dama ta ƙari lokaci da aka samu.
No comments