Daga Awwal Umar, Minna A ranar Litinin da ta gabata ne aka rantsar da sabon shugaban ƙaungiyar mahaddata Alƙur'ani ta ƙasa, reshen jihar...
Daga Awwal Umar, Minna
A ranar Litinin da ta gabata ne aka rantsar da sabon shugaban ƙaungiyar mahaddata Alƙur'ani ta ƙasa, reshen jihar Neja, a wani gagarumin bikin da aka gudanar garin Mina ta jihar Neja.
Gwani Hussaini Abubakar Shakwata, shi ne sabon shugaban da aka zaɓa bayan da ya kwashe watanni shida a matsayin na riƙo, bayan rasuwar Tsohon shugaban, Gwani Abubakar Maiturare.
Kimanin shekaru ashirin da uku da wata ɗaya ke nan da kafuwar wannan Ƙungiya ta 'Huffazul Qur'anin Kareem and Scholars Association of Nigeria', ƙungiyar da aka yi haɗakar wasu ƙungiyoyin makarantun tsangayu aka samar da ita don ƙarfafa makarantun tsangayu da ilmantar da Almajiran Allo sana'o'in hannu saboda yunƙurin Malaman na rage yawan barace-barace, da samun haɗin kai tsakanin Malamai da Hukumomin gwamnati.
Tun farko a bayaninsa, shugaban majalisar dattijai na ƙungiyar, Gwani Sani Isma'ila Maitunbi ya yaba wa shugabancin ƙungiyar da ya gabata saboda shirya tarukan saukar Alƙur'ani mai tsarki don yi wa ƙasa addu'o'in samun zaman lafiya, ba tare da sanya hannun gwamnati ba.
Gwani Sani Maitunbi, ya ce ƙungiyar an kafa ta ne kimanin shekaru ashirin da uku da wata ɗaya, wanda ta samu shugabanci mai adalci da ci gaba wajen haɗin kai, da sauƙaƙa wa gwamnati samun isar da pudurorin ta na inganta ilimin addini da yaƙi da barace-barace a wuraren da ba su dace ba.
A bayanin sa, mataimakin shugaban shugaban ƙungiyar da ya ripe matsayin har karo uku, Gwani Salihu Muhammad, ya ce a yanzu suna shirin fuskantar tantance yawan Almajiran tsangayu don ware Almajiran Alkur'ani mai tsalki da naƙasassu da kuma waɗanda suka mayar da bara sana'a.
A cewarsa hakan, zai bai wa ƙungiyar damar fuskantar ayyukan da ta sanya a gaba na inganta makarantun tsangaya da horar da Almajiran sana'o'in hannu daban-daban, don tsayuwa da pafarsu da kuma ci gaba da neman ilmin addini.
Shi kuwa Malam Sulaiman Yahaya Babangida, Cikasoron Minna, janyo hankalin Majalisar Dokoki ta ƙasa ya yi kan samar da dokokin da za su bai wa Almajiran Alkur'ani girm, kariya da mutunta Malaman Allo.
Basaraken ya ce, Malamai su ne fitilar al'umma, don haka ya zama wajibi waɗanda aka ɗora wa alhakin wannan jagorancin, su ji tsoron Allah, su sani Allah zai tambaye su kan wannan amanar da aka ba su.
Gwani Musa Adamu, shi ne shugaban ƙungiyar a yankin Arewa ta Tsakiya, wanda shi ya wakilci shugaban Ƙungiyar ta ƙasa, kuma ya jagoranci ƙaddamar da sabbin shugabannin.
A cikin jawabin sa, Gwani Musa ya janyo hankalin sabbin shugabannin akan aiki tuƙuru wajen haɗa kan Malamai lungu da saƙ, tare da rungumar manufofin gwamnat, muddin ba su saɓa wa karantarwar addini ba.
Ya ce, shugabancin ƙungiyar na ƙasa ya amince da wannan zaɓi, kuma yana sanya idanu akan irin rawar da za su taka, "muna da ƙalubale a kan barace-baracen ƙananan yara, muna da ƙalubale a kan yadda wasu Malamai ke jagorantar tsangayu. Donn haka Malamai su guji aikata duk wani abin da zai zama assha, domin su masu karantar da tarbiya ne," Gwani Musa.
Da ya ke jawabin kama aiki, sabon shugaban na jihar Neja, Gwani Husaini ya yaba wa gwamnatin jihar, bisa jagorancin manomi, Hon. Umar Mohammed Bago, bisa namijin ƙoƙarin da ya yi na janyo Malaman tsangaya a gwamnatinsa.
Ya ce, a bisa wannan ne har ƙungiyar ta samu muƙamin babban mai bada shawara a ɓangaren addini a ƙarƙashin Hukumar kula da addinai, bisa jagorancin Dr. Umar Faruq Abdallah, Sakataren ƙungiyar Limaman Juma'a, wanda kuma wannan shi ne irin sa na farko tun bayan dawowar mulkin Dimukuraɗiyya a tarihin jihar nan.
"Muna sa ran nan gaba kaɗan gwamnatin jihar Neja bisa sahalewar Majalisar Dokokin jiha za a kafa Hukumar kula da harkokin makarantun tsangaya, saboda irin gudunmawar da Malamai da Almajiran tsangayu ke bayarwa," in ji Gwani Husaini.
Ɗan Majalisar wakilai mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Chanchaga, Hon. Abubakar Audu Buba, ya sha alwashin ganin ya haɗa kai da wasu jami'an gwamnatin jiha don ganin an samar wa ƙungiyar sakatariya mai zaman kan ta don samun sauƙin gudanar da ayyukan ta yadda ya dace.
Bayan bayar da shaidar fara aiki ga sabbin shugabannin da za su yi wa'adin shekaru huɗu, an karrama wasu mutane da suka bada gudunmawa wajen haɗin kan 'ya'yan ƙungiyar don ci gaban ƙungiyar.
Daga cikin waɗanda aka karrama, akwai shugaban kwamitin kula da harkokin addinai na Majalisar Dokokin jihar Neja, Hon. Abdullahi Isah da Ɗan Majalisa mai wakiltar Kontagora ta biyu.
No comments