Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Mallakar Digiri Na Jabu: Ma'aikatar Ilimi Ta Haranta Karatu A Jami’o’in Kwatano, Togo Da Wasu A Nijeriya

Daga Musa Muhammad Ganin yadda ake samun mallakar Digiri ba bisa ƙa'ida ba, wanda kuma yawancin su na jabu ne, Ma’aikatar Ilimi ta Taray...

Daga Musa Muhammad

Ganin yadda ake samun mallakar Digiri ba bisa ƙa'ida ba, wanda kuma yawancin su na jabu ne, Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta dakatar da yin karatu a Jami'o'in ƙasashen Kwatano, Togo da wasu Jami'o'in a nan gida Nijeriya. 

A cikin waata sanarwa daga ma'aikatar ilimin, ta sanar da cewa ɗaukar wannan mataki ya biyon bayan wani bincike na sirri da wata kafar jarida ta yanar gizo a Nijeriya ta yi, wanda ya fallasa badaƙalar da ɗalibai da wasu Jami’o’in ke yi wajen mallaka wa ɗaliban takardar shaidar kammala Digiri, alhali babu cancanta.

Wani rahoto na baya-bayan nan, ahi ne ya nuna wani ɗan jarida ya samu Digiri a Jami’ar Kwatano a cikin makwanni shida kacal, kuma ya shiga cikin shirin hidimta wa ƙasa na shekara guda da Hukumar NYSC ke gudanarwa.

Wasu majiyoyin sun bayyana irin yadda wannan ɗan jarida ya kashe maƙudan kuɗaɗe, tun daga shiga Jami'ar har zuwa NYSC.

Ga jerin sunayen Jami’o’in ƙasashen waje da na gida Nijeeiya, waɗanda Hukumar Kula da Jami’o’i ta ƙasa (NUC) ta haramta kararu a cikin su, kamar yadda hukumar NUC ta bayyana a shafinta na yanar gizo:

1. Jami’ar Kimiyya da Gudanarwa ta Port Novo, Jamhuriyar Benin, da sauran cibiyoyin ta da ke Nijeriya.

2. Jami’ar Volta, da ke Ghana, da sauran cibiyoyin ta a Nijeriya.

3. Jami'ar International University, Missouri, USA, Kano da Lagos, da duk wasu cibiyoyin ta a Nijeriya.

4. Jami’ar Collumbus, UK, tana aik.da duk wasu cibiyoyin ta a Nijeriya

5. Tiu International University, UK, da duk wasu cibiyoyin ta a Nijeriya.

6. Jami’ar Pebbles, UK, da duk wasu cibiyoyin ta a Nijeriya.

7. London External Studies UK, da duk wasu cibiyoyin ta a Nijeriya.

8. Pilgrims University da duk wasu cibiyoyin ta a Nijeriya.

9. Jami’ar Kirista ta Yammacin Afirka, da duk wasu cibiyoyin ta a Nijeriya.

10. EC-Council University, USA, Ikeja Lagos Study Centre.

11. Concept College (London), Ilorin, da duk wasu cibiyoyin ta a Nijeriya.

12. Jami’ar Houdegbe ta Arewacin Amurka da ke Nijeriya.

13. Makarantar Kasuwanci ta Jami’ar Irish a London, da duk wasu cibiyoyin ta a Nijeriya.

14. Jami’ar Ilimi, Winneba, Ghana, da duk wasu cibiyoyin ta a Nijeriya.

15. Jami’ar Cape Coast, Ghana, da duk wasu cibiyoyin ta a Nijeriya.

16. African University Cooperative Development, Cotonou, da duk wasu cibiyoyin ta a Nijeriya.

17. Jami’ar Yammacin Pacific, Denver, Colorado, da ke da Cibiya a Owerri.

18. Jami’ar Evangel ta Amurka da Chudick Management Academic, Legas.

Binciken Matattarar Labarai ya gano cewa tun ba yau ba ake ta cece-kuce a kan yadda matasan ƙasar nan ke tafiya Kwatano suna kammala karatun Digiri cikin ɗan ƙanƙanin lokaci, wanda kuma daga bisa aka nuna cewa Ma'aikatar Ilimi ta tarayya ta tantance wasu, ta tabbatar da ingancin su. 

Sai dai yanzu bisa wannan sanarwa, ba a san ko ma'aikatar ilimin za ta fito ta wallafa sunayen Jami'o'in da ta amince ta su ba. 

 

No comments