Daga Awwal Jibril 'Yankara A Ranar Lahadi, 31 ga watan Disamba 2023, Matasa masu amfani da kafafen sadarwar zamani na Ƙaramar Hukumar F...
Daga Awwal Jibril 'Yankara
A Ranar Lahadi, 31 ga watan Disamba 2023, Matasa masu amfani da kafafen sadarwar zamani na Ƙaramar Hukumar Faskari da ke Jihar Katsina suka gudanar da taron sada zumunci na ƙafa-da-ƙafa a cikin garin Faskari, inda a suka karrama wasu daga cikin fitattun mutane masu taimakawa wajen ci gaban Ƙaramar hukumar.
Cikin jawabin sa a wurin taron, Ɗan Majalisa Mai Wakiltar Ƙaramar Hukumar Faskari, Injiniya Samaila Ma'azu Bawa Faskari ya yi kira ga masu son karrama mutane da su rinƙa tsayawa su natsu su ga me Mutum ya yi wa al'umma, ba kawai daga ya sami wata kujera ba, sai a hau rubibin karrama shi.
Shi ma a na sa jawabin, Shugaban Ƙaramar Hukumar Faskari, Hon Musa Bala Ado kira ya yi ga matasan da su guji bayar da labarin da ba su ji ba, ba su gani ba. Ya ce, saboda irin waɗannan Labaran na maida Ƙaramar Hukumar ta Faskari Baya.
Ya ce, "Mun sani muna cikin matsalar tsaro, amman wasu na kambama lamarin fiye da yadda yake."
Shi kuwa Malam Ibrahim Musa kira ya yi ga Matasan su ji Tsoron Allah, su sani duk abin da mutum ya rubuta sai an tambaye shi a kan sa.
Ciki Waɗanda da aka karrama, har da babban Likitan da ke zuwa duba marasa lafiya da kuma tiyata a babban asibitin garin na Faskari, Dr Yakub Salihu Funtuwa.
Sauran sun haɗa da Iljiniya Samaila Ma'azu Bawa, Ɗan Majilisa Mai Wakiltar Ƙaramar Hukumar Faskari a Majilisar Dokokin Jihar Katsina. Sai Hon. Musa Bala Ado, Shugaban Ƙaramar Hukumar Faskari. Sai Hon. Jamilu Muhammad Lion Ɗan Majilisar wakilai ta tarayya da ke Abuja Mai wakiltar Ƙananan Hukomomin Ƙanƙara, Faskari Da Sabuwa, Injiniya Aminu Umar Saidu Hakimin Faskari.
Akwai kuma Alhaji Sani Idiris Sambo, Hakimin Mairuwa, Hon. Hamza Suleman, Kwamishinan Ruwa na Jihar Katsina, da Alhaji Usaini Na Umma Jagaban Faskari, da Injiniua Aminu Barau Mairua, da Injiniya Shehu Sallau 'Yankara, Barayan Faskari, da Alhaji Ahmad Musa Wafa, Ɗanmalikin Faskari, da Injiniya Murtala Sheme Da Sauran su.
Shugaban Ƙaramar Hukumar Faskari, Hon. Musa Ado ne ya miƙa wa Likitan shaidar yabon, a madadin matasan.
Kowanne cikin waɗanda aka karrama sai da aka faɗi irin alkhairin da ya kawo ma Ƙaramar Hukumar ta Faskari.
A gurin taro, masana ne da dama suka yi bayani da nasihohi akan ta'amulli da kafar Sada zumunta, a ciki har da M.Ashiru Labbo Yankara, M.Ibrahim Musa Liman Faskari, da M. Abdulshahid Mahmud Inuwa da dai Sauran su.
No comments