Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Bidiyon Da Ake Yaɗawa, Na Sambisa Ne, Ba Jihar Filato Ba – Hedikwatar Tsaro

Hedikwatar Tsaron Nijeriya ta musanta rahotonnin da ake yaɗawa ta wani bidiyo a shafukan sada zumunta, inda nuna dakarun ta cin zafarin wasu...

Hedikwatar Tsaron Nijeriya ta musanta rahotonnin da ake yaɗawa ta wani bidiyo a shafukan sada zumunta, inda nuna dakarun ta cin zafarin wasu mata, aka alaƙanta abin da jihar Filato. 

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Hedikwatar, Birgediya Janar Tukur Gusau ya fitar, ta tabbatar da cewa sojojin Nijeriya ne a bidiyon, amma ba a Filato abin ya faru ba, kamar yadda wasu ke yaɗawa.

Ya ce, “Haƙiƙanin gaskiya, lamarin ya faru ne a Dajin Sambisa a shekarar 2021, kuma matan wasu ne daga cikin abokan zaman mayaƙan Boko Haram ne a lokacin da aka kama wasu daga cikin garuruwan su.”

Janar Gusau ya ƙara da cewa, tuni rundunar ta bincika, kuma ta hukunta waɗanda suka aikata hakan, saboda sun nuna rashin ƙwarewar aiki”.

Wasu daga cikin masu yaɗa bidiyon na nuna cewa lamarin ya faru ne a yankunan Bokkos da Barkin Ladi na jihar Filato bayan ‘yan bindiga sun kai hare-hare tare da kashe mutum kusan 200 lokacin bikin Kirsimeti.

“Muna kira ga masu yaɗa wannan bidiyo da su daina yin hakan saboda yana ƙara ta’azzara ƙalubalen tsaron da ake ciki, wanda kuma rundunar Operation Safe Heaven ke ƙoƙarin daƙilewa,” a cewar sanarwar.

 

No comments