Daga Hussaini Yero Tsohon Gwamnan jihar Zamfara, kuma Sanata mai wakiltar Mazaɓar Zamfara ta Yamma, Sanata Abdulaziz Yari Abubakar (Shattim...
Daga Hussaini Yero
Tsohon Gwamnan jihar Zamfara, kuma Sanata mai wakiltar Mazaɓar Zamfara ta Yamma, Sanata Abdulaziz Yari Abubakar (Shattiman Zamfara) ya bayyana rasuwar dattijo a jihar, Ambasada M. Z Anka a matsayin babban rashi ga ɗaukacin al'ummar Nijeriya, domin rashin tamkar wani gurbi ne mai wuyar cikewa.
Shugaban Kwamitin yaɗa labarai na Sanatan, Hon. Ibrahim Ɗan Madamin Birnin Magaji ne ya bayyana haka a sanarwar da ya sanya wa hannu, ya raba wa manema labarai a Gusau.
Sanata Abdulaziz Yari ya ce, "Magajin Garin Anka, kuma Jakadan Nijeriya a Libya ya yi wa Zamfarawa ƙoƙarin, musamman wajen fafutukar neman 'yancin kai har aka samu Jihar Zamfara a ranar 1 ga Oktoba, 1996."
Da yake jajanta wa ‘yan uwa, Masarautar Anka, Gwamnati da Al’ummar Jihar Zamfara bisa rashin wannan babban haziƙin ɗan siyasa kuma Jagora, Sanata Abdulaziz Yari Abubakar ya roƙi Allah SWT ya gafarta masa kurakuransa, ya kuma saka masa da gidan Aljanna.
Ambasada M. Z Anka ya rasu ne a ranar Juma’a 29/12/2023 sakamakon rashin lafiya, yana da shekaru 81, ya bar mata 2 da ‘ya’ya 13 da kuma jikoki da dama. Tuni dai aka yi jana’izar sa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
No comments