Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

NAHCON Ta Ƙara Lokacin Biyan Kuɗin Hajji Na Bana

  Hukumar kula da jin daɗin Alhazai ta Ƙasa, NAHCON ta sanar da ƙarin lokacin da aka tsayar don karɓar kuɗin aikin Hajjin bana, yanzu an san...

 

Hukumar kula da jin daɗin Alhazai ta Ƙasa, NAHCON ta sanar da ƙarin lokacin da aka tsayar don karɓar kuɗin aikin Hajjin bana, yanzu an sanya 31 ga watan Janairun 2024, maimakon ƙarshen watan da ya gabata na Disamba. 

Wannan ƙarin wa'adi ya na ƙunshe ne cikin wata samarwa da mai magana da yawun Hukumar, Fatima Sanda Usara ta sanya wa hannu.

Fatima ta ce, “an tsawaita wa’adin ne sakamakon kiraye-kirayen da Malaman addini, Hukumomin kula da jin daɗin Alhazai na Jihohi, Gwamnonin Jihohi da sauran masu ruwa da tsaki suka yi.”

Ta kuma bayyana cewa, amincewar da gwamnatin tarayya ta yi na tsawaita wa’adin ya ba da dama ga maniyyata su bayar da himma wajen biyan kuɗin kafin lokaci ya ƙure.

No comments