Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Samar Da Tsaro A Zamfara: An Ƙaddamar Da Jami'an Sa-kai Na (Askarawan Zamfara)

-Gwamnonin Arewa Maso Yamma Sun Halarta Daga Musa Muhammad Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya karɓi baƙuncin Gwamnonin yankin Arewa maso ...

-Gwamnonin Arewa Maso Yamma Sun Halarta

Daga Musa Muhammad

Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya karɓi baƙuncin Gwamnonin yankin Arewa maso Yamma a bikin ƙaddamar da jami'an tsaron da gwamnati ta kafa don samar da tsaro, wanda ake yi wa laƙabi da 'Askarawan Zamfara'. 

Taron ya gudana ne yau Laraba a harabar dandalin kasuwar duniya da ke Gusau, wanda ya samu halartar Gwamnonin jihohin, Jigawa, Kebbi, Kaduna, Kano, Katsina da Sakkwato. 

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya sanya wa sannu, ya bayyana cewa gwamnatin Zamfara ta ɗauki hanyoyi da salo daban-daban don kawo ƙarshen matsalolin tsaron da suka addabi jihar, na yanzu da kuma na nan gaba. 


Idris ya ce, “A bara, Gwamna Dauda Lawal ya amince da ɗaukar jami'an sa-kai guda 5,200 daga Ƙananan Hukumomin jihar 14. Yanzu kuma an yaye guda 2,645 a kashi na farko. 

Cikin jawabin da ya gabatar wajen bikin ƙaddamar da jami'an, Gwamna Dauda Lawal ya yi nuni da cewa, gwamnatin sa ta sadaukar da kanta wajen ganin ta sauke nauyin da ta ɗauko a duk fannonin ci gaban tattalin arziki da rayuwar jama'a. 

“Yayin da muke yin waɗannan ƙoƙari, manyan manufofin da muke da burin cimmawa ba za su kasance ba muddin ba a magance babban ƙalubale na rashin tsaro ba.

“Wannan ya sa muka yanke shawarar kafa Jami’an Tsaron Sa-Kai, waɗanda ake yi wa laƙabi da 'Askarawan Zamfara'. Kwamitin gudanarwa na kafa jami'an ya ratsa ƙananan hukumomin 14 tare da tantance masu aikin.

“Mun yi imanin cewa galibin ƙalubalen da muke fuskanta a matsayin mu na jiha da yanki sun samo asali ne daga tsananin sakaci wajen ciyar da manufofin jama’a don biyan buƙatun zamantakewar al’ummar mu. Ba za mu taɓa yin wasa da aikin al’ummar jihar mu ta hanyar ƙuri’unsu na watan Maris 2023 ba.

“Saboda haka, a yau rukunin farko na Askarawan 2,645, ne aka yaye. Waɗannan ma’aikat, matasa, masu kuzari da ƙwazo sun sami horo mai tsauri, da aikin yadda za su kare al'umma, da fahimtar ƙa’idojin aiki, da dai sauransu, wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansu na haɗin gwiwa, taimako da aiki tare da hukumomin tsaro don kare al’ummomin mu."

A nasa jawabin, Dakta Dikko Umar Radda, gwamnan jihar Katsin, kuma shugaban gwamnonin Arewa maso Yamma, ya jaddada matsayar su ta haɗin gwiwa na ƙin sulhu da ‘yan bindiga.

“Mun hallara a nan ne a yau da manufa guda: mu haɗa kai don yaƙar ’yan fashin daji da rashin tsaro a yankin Arewa maso Yamma, ba tare da la’akari da bambancin siyasa ba, mun ƙuduri aniyar cewa ba za mu taɓa yin sulhu da ‘yan bindiga ba.

A nasa jawabin, shugaban Jami'an Sa-Ka, Janar Aliyu Muhammad Gusau (Mai Ritaya) ya yaba wa gwamnatin jiha bisa kafa wannan rundunar.

No comments