Daga Musa Muhammad Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana cewa a duk faɗin Nijeriya, yankin Birnin Gwari mai fama da matsalar tsaro ne yankin d...
Daga Musa Muhammad
Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana cewa a duk faɗin Nijeriya, yankin Birnin Gwari mai fama da matsalar tsaro ne yankin da ya fi kowanne yanki yawan Albarkatun Ma'adanai ƙasa, sama da shekaru 100 da suka gabata.
Bayanin Hakan Ya fito ne daga Bakin Shugaban Kamfanin bunƙasa Albarkatun Ma’adanai na jihar Kaduna, Dakta Mohammed Nura Sani Hussaini, a zantawar sa da wakilinmu, inda ya ce tuni Gwamnatin jihar ta fara Nemo masu saka hannun Jari a ɓangaran domin bunƙasa tattalin arzikin jihar baki ɗaya.
Shugaban ya ce, sama da shekaru 100 da suka gabata babu irin nau'in Ma'adanan da babu a Birnin Gwari, rashin tsaro ya Sanya an bar su kara zube, wanda yanzu suke ƙoƙarin farfaɗo da su.
Ya ƙara da cewa yanzu Gwamnatin jihar Kaduna ta duƙufa wajen ɗaukar matakan tsaro a yankin domin samun Daman haƙo Ma'adanan wanda zai taimaka wajen inganta rayuwar al'umma baki ɗaya, a cewarsa, har an fara samun sauƙin kai hare-hare a yankin.
Shugaban ya ƙara da cewa, tuni manyan kamfanonin haƙar ma’adanai suka nuna sha'awarsu ta shigowa yankin domin fara haƙar ma’adanai, wanda nan gaba kaɗan za a buɗe yankin domin fara aiki gadan-gadan.
Ya ce har yanzu Gwamnatin jihar Kaduna ba ta bayar da lasisin haƙar ma’adanai a Birnin Gwari ba, Yana mai cewa, duk wanda yake aiki a yankin, to sojan gona ne.
Akan hakan, ya nuna rashin Jin daɗinsu dangane da yadda ake yawaitar samun masu haƙar ma’adanai a yankin ba bisa ƙa'ida ba, wanda suke taimaka wa wajen gurɓata tarbiyyar matasan yankin.
No comments