Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamna Lawal Ya Ayyana Dokar Ta-ɓaci A Fannin Kiwon Lafiya A Zamfara

Gwamna Dauda Lawal ya bayyana sanya dokar ta-ɓaci a fannin kiwon lafiya a Jihar Zamfara, tare da yin alƙawarin sake fasalin tsarin kiwon laf...



Gwamna Dauda Lawal ya bayyana sanya dokar ta-ɓaci a fannin kiwon lafiya a Jihar Zamfara, tare da yin alƙawarin sake fasalin tsarin kiwon lafiyar a duk faɗin jihar.
 
A wani jawabi da ya yi a faɗin jihar a ranar Talata, gwamnan ya koka da yadda yanayin asibitocin jihar Zamfara su ke.
 
Wannan bayani ya na ƙunshe ne a ciki wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar, inda ya bayyana cewa wannan sanarwar ta biyo bayan ziyarar ba-zata da gwamnan ya kai babban asibitin gwamnatin jihar da ke Gusau.
 
A cewarsa, asibitocin na buƙatar agajin gaggawa saboda rashin kyawun kayan aiki da da ma’aikata. Sakamakon haka an kafa dokar ta-ɓaci a fannin.
 
Sanarwar ta ƙara da cewa: “A yau, a wani shirin watsa labarai na jihar, Gwamna Dauda Lawal ya kafa dokar ta-ɓaci a ɓangaren kiwon lafiya na Zamfara.
 
“Ziyarar da Gwamnan ya kai babban Asibitin Gusau a daren Lahadi ne ya sa aka yanke wannan shawarar.
 
Gwamna Lawal ya nuna damuwarsa kan halin da majiyyata ke ciki a asibitoci, ya kuma bayyana irin matakan da gwamnatin sa ta ɗauka.
 
“A ranar Lahadi, 28 ga Janairu, 2024, na kai ziyarar ba-zata zuwa babban asibitin Gusau domin duba halin da yake ciki. Na yi mamaki kuma na shiga da damuwa game da yanayin da na tarar da irin halin da marasa lafiya ke cika na neman kulawar likita.

“Ba kawai lalacewar ababen more rayuwa ne ke shafar harkokin kiwon lafiya a jihar Zamfara ba, har ila yau yanayin aiki na ma’aikatan kiwon lafiya da jin daɗin su na da matuƙar tada hankali.

“A matsayinmu na gwamnati mai alhaki, muna ɗaukar matakan gaggawa don gyara al'amura.

“Bayanin yaƙin neman zaɓe na ya bayyana muhimman matsalolin kiwon lafiya da jihar Zamfara ke fuskanta. Waɗannan al'amurra suna da muhimmanci ga jin daɗi da ci gaban 'yan ƙasarmu. Na sadaukar da kai wajen magance su cikin gaggawa da kulawar da suka cancanta.

“Ɓangaren kiwon lafiya a Zamfara na fama da matsaloli da dama, da suka haɗa da ƙarancin kuɗaɗe da ingancin kiwon lafiya, tun daga ababen more rayuwa zuwa ayyukan kiwon lafiya.

“An yi asarar rayuka da dama a dalilin haka. Ina bayyanawa a yau cewa ba za mu ci gaba da ƙoƙarin saita komai.

“Don inganta fannin kiwon lafiya a jihar Zamfara, gwamnatina za ta fara gudanar da ayyuka kamar haka:

“Za mu inganta dukkan asibitocin gaba ɗaya ta hanyar bunƙasa ababen more rayuwa, da samar da na’urorin kiwon lafiya na zamani, da kafa ɗakunan gwaje-gwaje masu inganci.

“Za mu samar da kula da lafiyar mata da yara kyauta domin rage cutuwa da mace-macen mata da ƙananan yara.

“Za mu ba da kulawa ta musamman ga Cibiyoyin Kiwon Lafiya na Matakin Farko (PHCs) wajen samar da daidaitattun isar da kiwon lafiya a matakin farko ga al’ummomin da ke nesa.

“Za mu ɓullo da wani tsari na inganta walwala da jin daɗin duk ma’aikatan kiwon lafiya a jihar.

“Za mu kafa tsarin inshorar lafiya mai rahusa kuma mai inganci, tare da samar da ingantattun ayyukan kiwon lafiya ga ɗaukacin al’ummar jihar Zamfara.

“Za mu raba kayan aiki da magunguna masu muhimmanci ga dukkanin asibitocin da ke faɗin ƙananan hukumomi 14.

"Za mu yi aikin tantancewar jiki ta tilas ga dukkan ma'aikatan asibiti, gami da ma'aikatan wucin gadi. Kwamishinan lafiya na jihar zai kafa hanyar da ta dace ta kula da ma’aikatan da ke bakin aiki.

No comments