- Ya ce ilimi na gaba da komai Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana ilimi a matsayin ginshiƙi wajen gina al’umma masu nagarta. ...
- Ya ce ilimi na gaba da komai
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana ilimi a matsayin ginshiƙi wajen gina al’umma masu nagarta.
Gwamna Lawal ya bayyana muhimmancin ilimi ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a wajen taron yaye ɗalibai karo na 43 na Jami’ar Ahmadu Bello Zariya. A bikin da aka yi a ranar Asabar, an ba wa ɗalibai 25,432 da suka kammala karatun digiri lambar yabo.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta bayyana cewa gwamna Lawal tsohon ɗalibin jami’ar Ahmadu Bello ne kuma ya bayar da gudunmawa sosai ga jami’ar.
Ya ce gwamnan Zamfara ya bayar da gudunmuwa ga cibiyoyin ilimi daban-daban a ciki da wajen jihar Zamfara saboda kishinsa na bunƙasa ilimi.
Ya ce, “A yau, Gwamna Dauda Lawal ya halarci taron karo na 43 na Jami’ar Ahmadu Bello Zariya.
“Tun lokacin da ya ke aikin banki, ya kasance mai kishin cigaban ilimi, kuma a kodayaushe l tunanin sa shi ne bayar da gudunmawa ga al’umma.
“Gwamna Lawal ya gina bene mai hawa uku wanda ya ƙunshi ɗakunan karatu da ofisoshi. Bugu da ƙari, ya ba da sabuwar motar bas ta Costa ga Sashen Kimiyyar Siyasa, inda ya kammala karatunsa."
A watan Nuwamban shekarar da ta gabata ne Gwamna Dauda Lawal ya kafa dokar ta-ɓaci kan harkokin ilimi a jihar Zamfara.
Kamar yadda sanarwar ta fito, gwamnatin Gwamna Lawal ta fara ginawa tare da gyara makarantu 245 a faɗin (ananan hukumomi 14 na jihar Zamfara; samar da tebura masu kujeru biyu ga ɗalibai, jimlar 9,542 a fadin makarantu a ƙananan hukumomi 14; kayan aikin da aka gina tare da gyara makarantu 245 tare da tebura 619 da kujeru 926 na malamai.
No comments