Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamnatin Zamfara Za Ta Raba Dabbobi Kyauta Ga Mata A Jihar

Daga Hussaini Yero Gwamnatin Jihar Zamfara ta kammala shirye-shiryen raba dabbobi kyauta ga mata a jihar. Kodinetan shirin Fadama III na jih...

Daga Hussaini Yero

Gwamnatin Jihar Zamfara ta kammala shirye-shiryen raba dabbobi kyauta ga mata a jihar.

Kodinetan shirin Fadama III na jihar Ismael Abubakar Ribe ne ya bayyana wa manema labarai haka a lokacin da yake amsa tanbayoyi a ofishinsa da ke Gusau.

Kodinetan ya yi bayanin cewa an zaɓo ƙungiyoyin manoma takwas ne daga kowace Ƙaramar Hukumar, amma Gusau inda aka zaɓo ƙungiyoyi goma sha shida saboda ita ce hedikwatar jihar da tafi yawan al'umma.

Ya ci gaba da cewa, tuni Gwamnan Jihar Dauda Lawal ya fara ƙaddamar da rabon takin da kayan noma kyauta a ƙananan hukumomin da nufin kai wa mutanen kai tsaye a ƙananan hukumomi su.

Su kuma mata za a raba masu awaki kyauta don rage wahalhalun da mata ke fuskanta a yanzu haka.

Kuma gwamnatin jihar Zamfara ta damu matuÆ™a da halin da mazauna karkara ke ciki musamman awannan lokacin, za a ba kowane  akuya 3, mace 2 da kuma namiji domin su ci gajiyar tallafin.

No comments