Kwamitin haɗin gwiwa na ƙungiyoyin matasan Arewa ya yi kira ga ’yan Majalisar Dokokin Nijeriya waɗanda al’ummar Arewa suka zaɓa da su ƙara n...
Kwamitin haɗin gwiwa na ƙungiyoyin matasan Arewa ya yi kira ga ’yan Majalisar Dokokin Nijeriya waɗanda al’ummar Arewa suka zaɓa da su ƙara nuna turjiya kan batun komawar sassan CBN da nufin mayar da hedikwatar FAAN daga Abuja, babban birnin tarayya, zuwa Jihar Legas.
Kwamitin ya bayyana hakan ne a wata sanarwar da ya fitar kuma ya raba wa manema labarai.
Kwamitin ya ce, "Muna miƙa babban yabo ga masu girma sanatoci da 'yan majalisar wakilai da suka fito suka nuna rashin amincewarsu da hukuncin baya-bayan nan dangane da batun mayar da wasu muhimman sassa daga babban bankin Nijeriya (CBN) da kuma yunƙurin maida wasu hukumomin gwamnati Legas. Hedikwatar Hukumar Kula da Jiragen Sama ta Nijeriya (FAAN) daga Abuja, Babban Birnin Tarayyar Nijeriya, zuwa Jihar Legas.
Rahotanni daga kafafen yaɗa labarai na nuni da cewa ƙungiyar Sanatoci da ‘yan Arewa suka zaɓa, waɗanda suke wakilta a majalisar wakilai sun yi watsi ra'ayin Gwamnatin Tarayya a kan lamarin.
"Gaggawar lamarin na bukatar daukar matakin gaggawa na majalisa don gyara
waɗannan lamura daga manufofin tsarin mulkin mu."
Kwamitin ya ƙara da cewa, "yayin da su ke amincewa da matsayar da waɗannan ‘yan majalisar suka ɗauka, ƙungiyoyin Matasan Arewa na son ci gaba da yin kira ga wakilan mu a Majalisar Dokoki ta kasa da su yi cikakken aikin su na sa ido na doka. A bisa tsarin tsarin mulkin ƙasa, kungiyoyin matasan Arewa suna kira ga wakilanmu a Majalisar Dokoki ta kasa da su gudanar da cikakken ayyukansu na sa ido na doka. Muna rokon su da su sanya wa Hukumar Zartar wa’adi na soke hukuncin da suka shafi sauya sheƙar ma’aikatun CBN da hedikwatar FAAN tare da ɗaukar matakan gyara."
No comments