Wani ɗan jarida mazaunin Kaduna, Andrew Ibrahim Mshelia, ya buƙaci 'yan siyasar Arewa da su mayar da hankalinsu wajen kawo ƙarshen ’yan ...
Wani ɗan jarida mazaunin Kaduna, Andrew Ibrahim Mshelia, ya buƙaci 'yan siyasar Arewa da su mayar da hankalinsu wajen kawo ƙarshen ’yan fashin daji da ta’addancin da ke addabar yankin, maimakon wasa da siyasa ko mayar hankali kan batun shirin mayar da wasu sassan CBN da FAAN zuwa Jihar Legas.
A cewarsa, abin damuwa ne irin yadda ‘yan ƙasar ba za su iya kwana da idanuwansu biyu a rufe saboda sace-sacen mutane, ta’addanci da sauran munanan ɗabi'u na zamantakewa.
Ya yi nuni da cewa, da a ce an daɗe ana jin muryar ‘yan siyasar Arewa, da an kawo ƙarshen ’yan fashin daji da ta’addanci ba tare da harbi ko ɗaya ba.
Ya ƙara da cewa, abin da gwamnatin yanzu ke buƙata a wannan lokaci shi ne ƙoƙarin haɗin gwiwa don sake gina Nijeriya.
No comments