Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Abun Fashewa Cikin Kayan Gwangwan Ya Yi Sanadin Mutuwar Mutum Shida A Borno

Wani abun fashewa ya kashe wasu almajiran wata makaranta huɗu tare da wasu mutum biyu da ba a gano su wane ne ba a Ƙaramar Hukumar Gubio da ...



Wani abun fashewa ya kashe wasu almajiran wata makaranta huɗu tare da wasu mutum biyu da ba a gano su wane ne ba a Ƙaramar Hukumar Gubio da ke Jihar Borno.

An ruwaito cewa, shugaban ƙaramar hukumar Alhaji Mali Gubio ne ya tabbatar mata da faruwar wannan lamari, ya ce abin ya fashe a wani kango da misali karfe 11 na safiyar Asabar.

"Duka mutanen da abin ya rutsa da su sun mutu, don haka ba za mu iya tabbatar da abin da ya faru ba, amma wani abun fashewa ne ya tashi a inda ake ajiye matattun ƙarafa."

"An gano gawar wasu almajirai hudu, da wasu manyan mutane biyu sai dai ba mu kai ga gane daga ina suke ba, babu kuma wanda ya zo ya ce 'yan uwansa ne," inji shi.

Tuni gwamnan jihar Babagana Umara Zulum ya haramta gwangwan a jihar saboda lalata kayan kwamnati da sunan gwangwan.

No comments