Ƙungiyar wayar da kai da tallafa wa 'yan Ɗariƙar Tijjaniya ta Nijeriya, 'Tijjaniya Grassroot Mobilization and Empowement Initiative ...
Ƙungiyar wayar da kai da tallafa wa 'yan Ɗariƙar Tijjaniya ta Nijeriya, 'Tijjaniya Grassroot Mobilization and Empowement Initiative of Nigeria (TIGMEN) ta yi kira da babbar murya ga Rundunar sojojin ƙasar nan da su gaggauta binciken harin da aka kai wa masu bikin Maulidi na Tudun Biri, tare da hukunta waɗanda suka kai harin.
TIGMEN ta bayyana haka ne a wani taron manema labarai da ta kira a ranar Larabar da ta gabata a ofishin ta da ke Kaduna, wanda shugaban ƙungiyar, Sayyadi Nasiru Shaikh Bello ya gabatar, tare da sauran shugabannin ta.
Haka kuma ƙungiyar ta yi kira da a kafa wani ƙwaƙƙwaran kwamitin da zai kula da raba taimako da gudumawoyin da ake samu don ganin abin ya kai ma waɗanda suka cancanta. Ta kuma yi kiran da cewa a tabbatar an raba wannan taimako da ake cikin adalci da tsare gaskiya.
Daga nan TIGMEN ta nemi da a sanar da sakamakon kwamitin da aka kafa don binciken wannan lamari, aƙalla makwanni biyu bayan kafa shi. Inda ta ce, wajibi ne a biya diyyar waɗanda suka rasa rayukan su a wannan hari.
Ƙungiyar ta kuma ƙalubalanci gwamnati, kan cewa ta fito fili su bayyana wa duniya matakan da ta ɗauka don kauce wa aukuwar wannan abu a nan gaba.
Tun farko a jawabin nasa, Sayyidi Nasiru ya bayyana cewa sun kafa wannan ƙungiya ta su ta TIGMEN ne don jawo hankali, wayar da kai, ilimantarwa, girmamawa da tallafa wa mabiya ɗariqar Tijjaniyya a duk faɗin Nijeriya.
No comments