Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Azabtarwa Da Wuta: Gwamnatin Zamfara Ta Yi Aƙawarin Hukunta Wace Ake Tuhuma

  Daga Hussaini Yero Gwamnatin Jihar Zamfara, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dauda Lawal, ta ɗauki alwashin hukunta Aisha Tsafe, wacce aka kama...

 

Daga Hussaini Yero

Gwamnatin Jihar Zamfara, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dauda Lawal, ta ɗauki alwashin hukunta Aisha Tsafe, wacce aka kama da azabtar da yarinya 'yar shekaru Goma sha Biyu, mai suna Safiya Tsafe, inda ta rinƙa ɗiɗɗiga mata Ledar da ta sanya a wuta.

Kwamishiniyar harkokin mata da jin daɗin al'umma ta jihar, Dr Nafisa Muhammad ce ta tabbatar da haka a lokaci da ta ziyarci Safiya Tsafe a inda ta ke jinya bayan aukuwar lamarin.

Wannan yana ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Jami'in yaɗa labarai na Ma'aikatar, Suleman Isa ya sanya wa hannu, ya raba wa manema labarai a Gusau. 

Sanarwar ta ce, "Gwamnatin jihar Zamfara ba za ta lamunci irin wannan cin zarafi ba, kuma nan ba da jimawa ba, za a gurfanar da matar da ake zargi a gaban kotu domin ta girbi abin da ta shuka.

“Gwamnatin jihar tare da haɗin gwiwar wasu ƙungiyoyi masu zaman kansu a jihar za su bi wannan shari’a domin ganin an hukunta matar da ake tuhuma aikata wannan mumunan laifin”.

Tun da farko, mahaifiyar Safiya, Malama Maryam Muhammad, ta roƙi gwamnatin jihar da ƙungiyoyi masu zaman kansu da su taimaka wajen bin haƙƙin ɗiyar tata.

Daga nan mahaifiyar Safiya ta gode wa Kwamishiniyar da wasu jami’an ƙungiyoyi masu zaman kansu da suka nuna damuwa kan abin da ya faru da yarinyar.

No comments