Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Majalisar Zartarwa Ta Cire Jami'o'i Da Kwalejoji Daga Tsarin ‘IPPIS’

An cire Jami'o'in Tarayya da Kwalejojin Ilimi daga Tsarin Biyan Ma'aikata (IPPIS). Majalisar Zartarwa ta Tarayya ce ta ba da ami...



An cire Jami'o'in Tarayya da Kwalejojin Ilimi daga Tsarin Biyan Ma'aikata (IPPIS).

Majalisar Zartarwa ta Tarayya ce ta ba da amincewar a taron da ta yi ranar Laraba a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Ministan Ilimi Farfesa Tahir Mamman ne ya bayyana haka a lokacin da yake yi wa manema labarai na fadar gwamnati bayani tare da wasu ministocin sakamakon taron Majalisar, ya kuma ce hakan zai fara aiki nan take.

A cewarsa, Majalisar Zartarwa ta ce, babu buƙatar shugabannin jami’o’in su riƙa barin aikin su don zuwa Abuja suna bibiyar al'amuran albashin ma’aikatan su.

Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ta daɗe tana takun-saka da Gwamnatin Tarayya kan cigaba da amfani da IPPIS wajen biyan malaman jami’o’in haƙƙoƙinsu.

Mataimakin shugaban ƙungiyar ASUU, Chris Piwuna, wanda ke da kwarin gwiwar kin amincewa da IPPIS zai bayar da misali da ‘yancin cin gashin kan jami’o’in a matsayin wani muhimmin abu, inda ya zargi ofishin shugaban ma’aikata da yin katsalandan a harkokin jami’o’in.

No comments