Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ta'addancin 'Yan Bindiga Ya Kusa Kawo Ƙarshe A Zamfara -Gwamna Lawal

Gwamnan jihar Zamfara, Dr Dauda Lawal ya kai ziyara a Ƙaramar Hukumar Zurmi, inda ya tabbatar masu da ƙudirin gwamnatin sa na kawo ƙarshen t...

Gwamnan jihar Zamfara, Dr Dauda Lawal ya kai ziyara a Ƙaramar Hukumar Zurmi, inda ya tabbatar masu da ƙudirin gwamnatin sa na kawo ƙarshen ta'addancin 'yan bindiga daga duk faɗin jihar. 

Wannan ya na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Kakakin Gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya sanya wa hannu, wanda ya ce Gwamnan ya kai wannan ziyara ce jiya Alhamis domin ya jajanta wa Masarautar Zurmi da al'ummar Ƙaramar Hukumar,  bisa harin baya-bayan nan da mahara su kai masu. 

Sulaiman Bala ya ce, Gwamnan ya yi wa al'ummar wannan Ƙaramar Hukuma ta Zurmi da sauran al'ummar jihar alƙwarin ce cikin yardar Allah aikin 'yan bindiga zai kawo ƙarshe. Inda ya yaba wa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu bisa ƙoƙarin sa na yaƙi da 'yan bindiga a jihar. 

Sanarwar ta Sulaiman Bala ta ci gaba da bayyana cewa, “A jajircewar sa ta dawo da zaman lafiya a Zamfara, Gwamna Dauda Lawal ya ziyarci Ƙaramar Hukumar Zurmi domin ya jajanta wa masarauta da al'ummar ta, tare da yin alƙawarin ƙara ɗaukar matakai don kare aukuwar irin wannan a nan gaba. 

“Mai martaba Sarkin Zurmi, Alhaji Bello Suleiman ne ya tarbi Gwamnan a fadar sa."

A lokacin da ya ziyarci sansanin sojojin Nijeriya da ke Ƙaramar Hukumar ta Zurmi kuwa, Gwamna Lawal ya yaba wa ƙoƙarin sojojin tare da ƙarfafa masu gwiwa. 

Gwamnan ya ce, “Muna jin daɗin taimakon da gwamnatin tarayya ke yi mana, musamman wajen ƙaro mana jami'an tsaro a wuraren da abin ya fi muni a sassan jihar nan. Jami'an tsaro na yin abin a yaba wajen kare rayuka da dukiyar al'umma."

Daga nan kuma sai Gwamman ya wuce, inda ya kai ziyara ga sansanonin 'yan gudun hijira da ke zaune a Kwalejin gwamnati ta GSS Zurmi, Kwalejin gwamnati ta GSS da ke Nasarawan Zurmi da kuma waɗanda ke a makarantar Firamare ta  Dauran.

A nan ne Gwamnan ya jajanta masu, tare da miƙa masu kayan tallafi. Ya kuma yi masu alƙawarin yin duk mai yiwuwa don ganin an mayar da su mahallen su, tare da tabbataf masu da aniyar sa ta ɗaukar matakan kawo ƙarshen wannan Ta'addanci. 

 

No comments