Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamna Dauda Lawal Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗi Na Naira Biliyan 423

Daga Musa Muhammad  Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya gabatar wa Majalisar Dokokin jihar Kasafin Kuɗin shekarar 2024, inda aka kasafta N...

Daga Musa Muhammad 

Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya gabatar wa Majalisar Dokokin jihar Kasafin Kuɗin shekarar 2024, inda aka kasafta N423,523,730,000.00.

Taken kasafin kuɗin na jihar Zamfara na shekarar 2024 shi ne, "Kasafin Ceton Al'umma", wanda kuma aka gabatar wa Majalisar a Alhamis ɗin nan a ginin Majalisar da ke Majalisar Dokokin jihar a Gusau. 

A cikin wata sanarwa da Mai magana da yawun Gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya sanya wa hannu, ya bayyana cewa kasafin ya ƙunshi N118,134,730,000.00 da aka ware wa ayyukan yau da kullum, sai kuma N305,389,000,000.00 da aka ware ma manyan ayyuka.

Sanarwar ta Sulaiman Bala ta ci gaba da cewa, gwamnatin jihar Zamfara za ta faɗaɗa ayyukan da ta ke gudanarwa a biranen jihar, za a buɗa su zuwa Ƙananan Hukumomin jihar 14 a kasafin na 2024.

“Yau Gwamna Dauda Lawal ya miƙa kasafin Kuɗin jihar ga Majalisar Dokoki, inda aka ƙiyasta za a kashe tsabar kuɗi har N423,523,730,000.00, wanda ayyukan yau da kullum za su kwashi N118,134,730,000.00, sannan an ware wa manyan ayyuka N305,389,000,000.00. 

“Wannan kasafin kuɗi ya yi la'akari da halin da al'ummar jihar Zamfara ke ciki, kuma an yi kyakkyawan tsari don biyan abubuwan da suka fi buƙata.

“Bugu da ƙari, wannan kasafin kuɗi, ba wai a tsarin kuɗi kawai aka mayar da hankali ba, akwai kyakkyawan tsarin sake gina jihar Zamfara don samar da alƙibla tagari. Muna nan a kan bakar mu na gudanar da kashe kuɗi ta hanyar da ta dace, babu ɓoye-ɓoye, komai zai zama a bayyane, musamman mu'amala da harkar kuɗi. 

"A wannan shekara ta 2024, gwamnatin jihar Zamfara ta tsara aiwatar da ayyuka masu dama, waɗanda suka haɗa da: Ci gaba da shirin gyaran birane; Gina hanya mai kilomita 17 ta Mallamawa zuwa Bukkuyum; Hanyar Bukkuyum zuwa Birnin Zauma zuwa Gummi; Hanyar Maradun zuwa Makera; Hamyar Damri zuwa Aje Wargi zuwa Dakko zuwa Rafin Gyero zuwa Barayar Zaki zuwa Nasarawar Burkullu; Hanyar Maradun zuwa Magami zuwa Faru; Hanyar Magami-Ɗangulbi-Ɗankurmi-Bagega zuwa Anka da dai sauran su da dama."

Sulaiman Bala ya ƙarƙare da cewa, wannan kasafin kuɗin ya mayar da hankali wajen ayyukan 'yan ƙasa, sannan wasu ayyukan kuma za su kasance na kai tsaye don biyan buƙatun Zamfarawa. 


 

No comments