Ƙungiyar Matasan Arewa ta bayyana amincewa da shugabancin Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewa (ACF), tare da jaddada cewa ƙungiyar ta shirya tsaf domi...
Ƙungiyar Matasan Arewa ta bayyana amincewa da shugabancin Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewa (ACF), tare da jaddada cewa ƙungiyar ta shirya tsaf domin samar da zaman lafiya, haɗin kai da samar da wadata a faɗin Arewacin Nijeriya baki ɗaya bisa ingantaccen tsari.
Gamayyar ƙungiyoyin matasan Arewa, kwamitin haɗin gwiwa na ƙungiyoyin matasan Arewa (JACOM), sun yi amanna da ƙungiyar tuntuɓa ta Arewa (ACF) domin ganin an samu sauyi tare da sauya akalar shugabancin ƙungiyar ta fannin zamantakewa da al’adun Arewacin Nijeriya.
Ƙungiyar Matasan Arewa, a wata sanarwa da Murtala Abubakar, shugaban JACOM da Israel Musa, Sakatarenta suka fitar ya bayyana cewa ci gaban da ƙungiyar ta ACF ta yi ya kan kama ns a makon da ya gabata yayin ƙaddamar da sabon kwamitin zartarwa na ƙasa don gudanar da harkokin ƙungiyar na tsawon shekaru uku masu zuwa bayan ƙarewar wa’adin tsohon ministan noma, Dattijo Audu Ogbe.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, "sauyin da aka samu cikin kwanciyar hankali da lumana ya biyo bayan yunƙurin da kwamitin zaɓe wanda ya samar da ƙungiyar zartaswa a halin yanzu a ƙarƙashin jagorancin Mamman Mike Osman SAN, shaida ce a sarari ga jajircewar ACF na tunkarar nauyin da ke kanta da sabbin dabaru da fa'idoji."
"Kwamitin haɗin gwiwa na ƙungiyoyin matasan Arewa yana da yaƙinin cewa bin bayanan mutanen da suka kafa sabuwar lungiyar zartaswa da aka ƙaddamar, da manufar kafa ƙungiyar ACF da dai sauransu, don samar da zaman lafiya da haɗin kai da samar da cigaba a faɗin ƙasa baki ɗaya."
"A yayin da muke sa ido kan manufofin shugabanci na yankin Arewa a halin yanzu, ƙungiyarmu ta tabbatar wa ACF cikakken jajircewarmu da ɗaukacin al’ummar Arewacin ƙasar nan a shirye muke mu hada kai da sabon kwamitin zartarwa na ACF ba wai don tabbatar da hadin kai ba kawai, amma sai don ƙara wa matasa kuzari da hikimar don tunkarar ƙalubale, sannna kuma don dawo da tsaro, zaman lafiya, hadin kai da ci gaba a yankinmu don fatan alheri da kuma don gobe, musamman a wannan mawuyacin lokaci", inji sanarwar.
Sanarwar ta ce, "muna kira ga ɗaukacin ‘yan Arewa ba tare da la’akari da harshe, addini, tsatson ko siyasa ba da su haɗa kai su baiwa ACF goyon bayan da take buƙata domin sauke nauyin da ke kanta."
No comments