Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya ƙaddamar da aikin gyaran Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Lafiya da ke Tsafe a ranar Juma’a a wani mataki...
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya ƙaddamar da aikin gyaran Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Lafiya da ke Tsafe a ranar Juma’a a wani mataki na sake farfaɗo a fannin ilimi a Jihar Zamfara.
Gyaran, wani ɓangare ne na shirin NG-CARES na Bankin Duniya don ƙarfafa al'umma ta hanyar gyara abubuwan da ake da su ta hanyar ayyukan ci gaban jama'a.
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ta ce, gyaran da aka yi na kwalejin kiwon lafiya shi ne na farko a jerin atisayen irin wannan da za a yi a wasu zaɓaɓɓun cibiyoyi a faɗin jihar.
A yayin jawabin da ya gabatar a wajen taron, sanarwar ta ƙara da cewa, Gwamna Lawal ya jaddada aniyarsa ta sake fasalin fannin ilimi a jihar.
“Muna da niyyar tabbatar da yin amfani da kuɗaɗen NG-CARES bisa tsarin Bankin Duniya domin a inganta cibiyoyinmu da kuma samar da ayyukan yi ga jama’armu.
“Tsarin da aka kafa a yau shi ne na farko cikin ayyukan jama’a da za a ƙaddamar a faɗin jihar. Yawancin makarantunmu, asibitoci, da hanyoyin karkara an zaɓo su ne don gyara su daidai da ƙa'idojin Bankin Duniya. A lokaci guda, wani muhimmin sashi na tallafin zai tafi ɓangaren musayar kuɗi.
“Ina da yaƙinin cewa ‘yan ƙasarmu za su yi amfani da wannan tsari na gaskiya kuma za su ci gajiyar sa, mu mutane ne masu himma da kwazo sosai kan masana’antu da kasuwanci, a matsayinmu na gwamnati mun himmatu wajen yin duk abin da za mu iya yi da ƙarfinmu da kuma ta hanyar da ta dace, da yardar Allah za a samar da yanayi mai dacewa don cigaban tattalin arziki a kowane amfani."
“Ina fatan aikin da aka fara yau a wannan harabar zai inganta ingantattun ababen more rayuwa a kwalejin don tallafa wa koyo da koyarwa da bincike. Mun ƙuduri aniyar gyara dukkan gine-ginen da suka lalace a cibiyoyinmu tare da samar da kayan karatu da kayan aikin da suka dace don amfanin yaranmu da kuma gobe mai kyau”.
No comments