Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

An Damƙe Matar Da Ta Daɓa Wa Matashi Wuƙa A Kano

Rundunar 'Yan Sanda a Kano ta kama wata matar aure mai suna Hafsat Sirajo mai shekaru 24 bisa zargin kashe wani matashi mai suna Nafiu H...



Rundunar 'Yan Sanda a Kano ta kama wata matar aure mai suna Hafsat Sirajo mai shekaru 24 bisa zargin kashe wani matashi mai suna Nafiu Hafizu da wuƙa.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Muhammad Usaini Gumel, ya gabatar da wadda ake zargin tare da wasu mutane biyu a gaban manema labarai a ranar Juma’a.

Gumel ya ce, Hafsat, wata mazauniyar Unguwa Uku da ke ƙaramar hukumar Tarauni, ta amsa laifin kashe mamacin ta hanyar daɓa masa wuƙa.

Ya ce an kama mijinta, Dayyabu Abdullahi mai shekaru 38 da kuma mai gadinsu Malam Adam mai shekaru 65 bisa laifin taimakawa wajen ɓoye gawar don ɓoye laifin kisan kai.

Hafsat ta shaida wa manema labarai cewa direban da ke zaune tare da su ya yi ƙoƙarin hana ta kashe kanta inda ya ƙwace wuƙa a hannunta.

“Na ɗan yanke a hannuna sai ya ce in je in canja tufafina. Ina fitowa daga banɗaki na hango shi kwance sai na ɗauki wuƙar na daddaɓa masa,” inji ta.

A halin da ake ciki, mahaifin marigayin, Malam Hafizu Gorondo, yana zargin cewa ma’auratan sun haɗa baki ne don kashe ɗansa saboda wasu maƙudan kuɗaɗe da yake bin mijin matar.

Ya ce ɗansa ya shaida masa gazawar Dayyabu wanda shi ma abokin kasuwancinsa ne ya biya shi bashin Naira miliyan 25m.

‘Yan sandan sun ce za a gurfanar da waɗanda ake zargin da zarar an kammala bincike.

No comments