Daga Musa Muhammad Mataimakin Shugaban Majalisar Dattijai ta tarayya, Sanata Barau Jibrin ya miƙa saƙon taya murnar sa ga al'ummar Kiri...
Daga Musa Muhammad
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattijai ta tarayya, Sanata Barau Jibrin ya miƙa saƙon taya murnar sa ga al'ummar Kiristocin duniya, musamman na Nijeriya bisa zagayowar ranar kirsimeti. Inda ya hore su da su sanya ƙasar nan cikin addu'a don samun zaman lafiya, haɗin kai da ci gaba mai amfani.
Sanata Jibrin ya miƙa wannan saƙo nasa ne ta hannun Kakakin sa, Alhaji Mudashir Ismail. Wanda ya yi kira gare su da cewa kada su manta da ainihin abin da kirsimeti ke koyarwa, su duƙufa da yi wa ƙasa addu'a.
Sanarwar ta Mudashiru ta kuma bayyana cewa, Sanatan ya jawo hankalin al'ummar Nijeriya kan su sanya aminci a zukatan su game da kyawawan shirye-shiryen inganta ƙasa na Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Shugaban Majalisar Dattawan ya ce, “Ina miƙa saƙon taya murna ta ga kiristoci, da ma sauran al'ummar Nijeriya na wannan lokaci na bikin kirsimeti na wannan shekara.
“Na hori mabiya addinin kirista su kasance masu riƙo da koyarwar Yesu Kiristi a duk al'amuran su na yau da kullum.
No comments