Daga Musa Muhammad, Kaduna Shugaban Gidauniyar 'Glovis Entrepreneurial and Leadership Development (GELD) Foundation', Gidauniyar da ...
Daga Musa Muhammad, Kaduna
Shugaban Gidauniyar 'Glovis Entrepreneurial and Leadership Development (GELD) Foundation', Gidauniyar da ta yi fice wajen tallafa wa jama'a, wato Mr Kayode Akinade, ya bayyana cewa babbar manufar wannan Gidauniya, ita ce sanya farin ciki da annashuwa a Zukatan zawarawa da iyalan su, musamman a lokacin bikin Kirsimeti.
Mr Kayode ya bayyana cewa ko a bana ma Allah ya ba su ikon bayar da wannan tallafi, inda a bara, mata 330 ne suka amfana da wannan tallafi nasu a jihohi 7, sannan a bana kuma, abin zai iya nunkawa.
Shugaban ya ce, "A shekarar nan ta 2023, mu na sa ran sanya farin ciki a fuskokin aƙalla zawarawa 500 da kuma tsofaffi 10 daga jihohin Kaduna, Kwara, Oyo, Abuja, Kano, Nassarawa, Filato, Edo, Benuwe da kuma Legas. Za mu tanadar masu da kayan abinci da kuɗaɗe a wannan lokaci na bukukuwan kirsimeti."
Haka kuma Mr Kayode ya yi nuni da cewa, a cikin tsarin wannan gidauniya, za su É—auki sunayen zawarawa da tsofaffi, inda za a É—auki adireshin su, sana'o'in su, matsayin karatun su, yanayin lafiyar su da sauran muhimman bayanai game da su.
Ya ce, gidauniyar G.E.L.D tana da jajircewa wajen ganin ta rage wa zawarawa da tsofaffi yanayin matsin rayuwa da su ke ciki, ta yadda za su sanya su cikin ayyukan hannu, kasuwanci da ƙananan sana'o'i don su samu abin dogaro da kan su.
No comments