Daga Musa Muhammad Ƙungiyar matasan Kiristoci (NCYP) da ke yankin Arewacin Nijeriya sun bayyana cikakken farin ciki da gamsuwarsu game da ab...
Daga Musa Muhammad
Ƙungiyar matasan Kiristoci (NCYP) da ke yankin Arewacin Nijeriya sun bayyana cikakken farin ciki da gamsuwarsu game da abin da Gwamnatin tarayya ta yi na bayar da tallafin sufuri da kashi Hamsin (50) cikin 100 a lokacin bukukuwan Kirsimati da na sabuwar Shekara da tallafin zai shafi waɗansu muhimman hanyoyi guda 22 a duk faɗin ƙasar.
Kamar yadda ƙungiyar ta bayyana cewa, cikin wata sanarwa da shugaban ta, Isaac Abrak ya sanya hannu, Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta nuna a fili cewa ta na aiwatar da dukkan ayyukanta ne domin ci gaban talakawan ƙasa, wanda hakan ya sa Ƙungiyar matasan Kiristoci ƙwararru a fannonin ilimi daban-daban mai suna NCYP suka bayyana godiyarsu da jin daɗin abin da Gwamnatin Gwamnatin aiwatar ta hanyar Sanya rayuwar talakawan kasa a cikin walwala da yanayi mai kyau.
"A matsayin mu na ƙungiyar Kiristoci ta NCYP muna taya ɗaukacin Kiristoci murnar samun hakan a duk faɗin ƙasa baki ɗaya. Saboda wannan cire tallafin zai taimaka wa Kiristoci su samu sukunin yin tafiye-tafiye domin aiwatar da bukukuwan kirsimati da na sabuwar shekara tare da iyalai, 'yan uwa da abokan arziki a duk faɗin ƙasar, " ta ce.
Daga nan Ƙungiyar na yi kira ga Kiristoci da sauran jama'a da su yi amfani da wannan dama domin cin moriyar shirin taimaka wa rayuwar jama'a da Gwamnatin tarayya ta fito da shi, wanda aka ware zai fara aiki tun daga ranar 21 ga watan Disamba, 2023, zuwa ranar 4 ga watan Janairu, 2024.
"Muna yin kira ga kowa da kowa da a yi tafiya cikin hankali kwanciyar hankali da lumana domin a samu damar yin Hutu tare da 'yan uwa, masoya da abokan arziki a lokacin wannan hutun kirsimati da sabuwar shekara lafiya, " in ji Ƙungiyar.
Bugu da ƙari kuma, Ƙungiyar ta ƙara bayar da ƙwarin gwiwa ga dukkan masu harkokin sufuri da aka zaɓa da za a yi wannan aikin bayar da tallafin sufuri da su, da suka haɗa da kamfanonin 'God is Good, Chisco Transport, Young shall Grow, God Bless Ezenata, Area Motors', da kuma hukumar kula da zirga-zirgar sufurin jirgin ƙasa ta Nijeriya ( NRC), muna yin kira a gare su cewa su tabbatar da cewa matafiyan da suka dace ne kawai na gaskiya suka samu cin mariyar shirin.
No comments