Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

KALAMAN BATANCI: Ƙungiyar 'Kano First Forum' Ta Kai Ƙorafi Kan Aminu Babba Ɗan Agundi

Daga Ibrahim Muhammad, Kano Wata ƙungiya mai suna 'Kano First Forum' ta kai ƙorafi ga Kwamishinan ‘Yan sandan Jihar Kano kan wasu ka...


Daga Ibrahim Muhammad, Kano

Wata ƙungiya mai suna 'Kano First Forum' ta kai ƙorafi ga Kwamishinan ‘Yan sandan Jihar Kano kan wasu kalamai da ta ce Alhaji Aminu Babba Ɗan Agundi ya yi, waɗanda ƙungiyar ke ganin na iya dagula zaman lafiya da haifar da tashin hankali a jihar.

A cikin ƙorafin da lauyoyin ta suka shigar, Kano First Forum ta nemi rundunar ‘Yan sandan Jihar ta gudanar da cikakken bincike cikin sirri da adalci domin gano haƙiƙanin abin da ya faru da kuma yanayin kalaman da ake zargin Alhaji Aminu Babba Ɗan Agundi ya yi.

Ƙungiyar ta ce kalaman sun fito ne a wani taron manema labarai da aka gudanar a ranar 1 ga Oktoba, 2026, bayan halartar Khalifa Muhammadu Sanusi II, Sarkin Kano, bikin ranar samun ‘yancin kan Nijeriya.

A cewar ƙorafin, taron manema labaran ya ta’allaƙa ne kan batun amfani da doki da Sarkin ya yi a yayin bikin, duk da cewa akwai umarnin gwamnatin Jihar Kano da ya shafi amfani da dawakai.

Sai dai abin da ya fi jawo hankalin ƙungiyar shi ne wani furuci da ta ce an danganta wa Aminu Babba Ɗan Agundi, inda ake zargin ya ce al’ummar Kano su “jira dawowarsu, su kuma jira ƙarin umarni daga gare su.”

Ƙungiyar ta bayyana cewa ƙorafin nata, ba wai ya shafi bambance-bambancen siyasa ko na masarauta kawai ba ne, sai dai damuwarta ta ta’allaƙa ne kan abin da ka iya biyo bayan irin waɗannan kalamai a halin da ake ciki.

Ta ce barin jama’a cikin rashin tabbas kan wanda ake nufi da “dawowa”, abin da dawowar za ta ƙunsa da kuma ma’anar “ƙarin umarni” na iya haifar da fargaba da tashin hankali ba tare da wata fa’ida ba.

Saboda haka  ta ce ta garzaya ga ‘Yan sanda ne domin a ɗauki matakan da suka dace na hana duk wani abu da ka iya kara dagula yanayin da ake ciki.

Sai dai Kano First Forum ta jaddada cewa matakin nata ba yunƙurin hana mutane bayyana ra’ayinsu, yin suka ko gudanar da muhawara bisa doka ba ne.

A maimakon haka, ta ce burinta shi ne ganin an magance dukkan batutuwan da suka shafi masarautar Kano ta hanyoyin doka da zaman lafiya, ba tare da jefa rayukan al’umma cikin hatsaniya ko barazanar rikici ba.

Ƙungiyar ta bukaci rundunar ‘Yan sandan Jihar Kano ta binciki lamarin tare da duba yanayin da aka furta kalaman, domin tantance ko sun karya wata doka ko kuma suna da damar kawo cikas ga zaman lafiyar jama’a.

Haka kuma, ta yi kira ga ‘yan siyasa, sarakuna, malaman addini da shugabannin al’umma da su rika taka-tsantsan wajen yin kalamai a bainar jama’a, musamman kan batutuwan da suka shafi masarautar Kano.

Kano First Forum ta ce Kano muhimmiyar jiha ce ta fuskar kasuwanci, zamantakewa da siyasa, don haka zaman lafiyarta na da muhimmanci ga miliyoyin mutane a ciki da wajen jihar.

“Duk wani sabani da ake da shi kan masarautar Kano, ya kamata a warware shi ta hanyar kotuna da sauran hukumomin da doka ta tanada, ba ta hanyar kalaman da za a iya fassara su a matsayin barazana, umarni ko kira ga yin fito-na-fito ba,” in ji kungiyar a cikin korafinta.

Ta ce za ta ci gaba da mara wa zaman lafiya, tsaron jama’a da bin doka baya, tana mai cewa korafin ya samo asali ne daga bukatar kauce wa duk wani rikici da za a iya hana shi tun kafin ya faru.

An aika kwafin korafin ga Sufeto-Janar na ‘Yansanda na kasa da kuma Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) domin su samu damar duba lamarin.

Kungiyar ta kuma bukaci hukumomin tsaro da su gudanar da bincike mai zaman kansa kan lamarin tare da daukar matakin da doka ta tanada, idan binciken ya nuna cewa akwai abin da ya dace a yi, domin kare zaman lafiya da tsaron jama’a a Jihar Kano.
 

No comments