Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

SHEKARA UKUN CARDOSO A CBN: Mun Gaji Gundarin Dala Miliyan 859 A Asusun Kuɗaɗen Waje, Yanzu Kuwa Ya Cika Maƙil Da Dala Biliyan 40 - CBN

  Daga Ashafa Murnai Barkiya Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya bayyana cewa har kusan ƙarshen 2023, adadin dalolin da ke asusun kuɗaɗen wajen ...


Daga Ashafa Murnai Barkiya

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya bayyana cewa har kusan ƙarshen 2023, adadin dalolin da ke asusun kuɗaɗen wajen Nijeriya bai wuce dala miliyan 859 kacal ba.

Wannan a cewar bankin ya nuna a 2023 an samu gagarimin koma-baya da aka samu wanda ba a taɓa samun irin sa a tarihin CBN.

 CBN ya ƙara da cewa ƙanƙantar adadin a wancan lokaci ya yi ƙasa da kuɗin da ake buƙata wajen biyan kuɗin shigo da kaya na ƙasa da wata ɗaya.

CBN ya ƙara da cewa bayan shekaru uku darajar asusun ta sake ɗagawa cike maƙil zuwa dala biliyan 40 a ƙarƙashin jagorancin Gwamnan CBN na yanzu, Olayemi Cardoso.

Mataimakin Gwamnan CBN Mai Kula da Ayyukan Kamfanoni, Dr. Muhammad Abdullahi, ne ya bayyana hakan a wajen buɗe taron ƙara wa juna sani karo na 38 na Ƙungiyar Masu Rubuta Labaran Harkokin Kuɗi da Editocin Harkokin Kasuwanci, wanda aka gudanar cikin makon juya Abuja jiya.

Ya ce shugabannin da suka karɓi ragamar CBN a shekarar 2023 a ƙarƙashin Cardoso, ta tarar da matsaloli masu yawa, kuma dole ta aiwatar da sauye-sauye daban-daban domin magance su yadda ya kamata.

Ya ce:
“Ya zuwa shekarar 2023, kasuwar canjin kuɗin waje ta Nijeriya ta kasance a rarrabe sosai, inda ake da bambance-bambancen farashi daban-daban na musayar kuɗi, tare da wata babbar kasuwar bayan fage."
 
Ya ce wannan ya sa ya yi matuƙar wahala ga ’yan kasuwa su san wane farashin canji ne za a yi amfani da shi ko kuma lokacin da za a samu kuɗin waje.

“Bambancin da ke tsakanin farashin hukuma da na kasuwar bayan fage ya kai matsakaicin sama da kashi 60 cikin 100 a shekarar 2022, sannan ya wuce kashi 100 cikin 100 a wasu lokuta daga baya a waccan shekarar.

“Domin a fahimci girman lamarin, Bankin Duniya ya kiyasta cewa tallafin ɓoye da tsarin farashin canjin kuɗin ya haifar ya janyo wa ƙasar asarar kusan kashi uku cikin 100 na  Gejin Ƙarfin Tattalin Arzikin Cikin Gida (GDP) a shekarar 2022.

“Matsin lambar ya kuma shafi ajiyar kuɗin waje na ƙasar nan. Adadin ajiyar kuɗin waje gaba ɗaya bai bayar da cikakken bayanin halin da ake ciki ba. Bayan cire wasu sanannun basussuka da wajibai na ɗan gajeren lokaci, bayanan CBN sun nuna cewa ajiyar kuɗin waje da za a iya amfani da ita kai tsaye ta tsaya a dala miliyan 859 a rubu’i na biyu na shekarar 2023.

“Haka kuma, basussukan da suka taso daga yarjejeniyoyin saye da sayar da kuɗin waje sun haura dala biliyan 7, lamarin da ya ƙara rashin tabbas ga da yin kaffa-kaffar da ’yan kasuwa da masu zuba jari suka riƙa yi da Nijeriya.

“A lokaci guda, jarin da ke shigowa ƙasar nan ya ragu, yayin da rashin tabbas game da samun kuɗin waje ya sa ya yi wahala ga ’yan kasuwa su tsara farashin kayayyaki, shirya zuba jari da kuma cika wasu wajibcin su.

“Kowace matsala ta ƙara jawo wata. Tsarin rabon kuɗin waje ta hanyar umarnin gwamnati ya raunana siginar da farashi ke bayarwa, tare da samar da damar yin amfani da bambancin farashi domin samun riba ba bisa ƙa’ida ba."

 Ya ce yawan kuɗin da ke yawo a cikin tsarin ya ƙara matsin lamba a kasuwar kuɗin waje.

“Daga nan kuma rashin tabbas ya sa ƙarin harkokin kasuwanci suka koma daga kasuwar hukuma, abin da ya ƙara raunana amincewa da tsarin.”

Ya ce waɗannan matsaloli ne suka zama tushen sauye-sauyen da CBN ya aiwatar a cikin shekaru uku da suka gabata.

Ya ce:
“Kasuwar kuɗin waje tana buƙatar farashi mai bayyana a sarari da kuma ingantaccen tsarin hada-hadar kuɗi, amma zai yi wuya a ɗore da waɗannan sauye-sauye ba tare da tsaurara kula da yawan kuɗin da ke cikin tsarin ba.

“Haka kuma muna buƙatar bankuna masu ƙarfi waɗanda za su iya gudanar da ayyukan su yadda ya kamata yayin da ake aiwatar da waɗannan sauye-sauye. Wannan shi ne tunanin da ya jagoranci sauye-sauyen da suka biyo baya.
 

No comments