Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamnan Bauchi Ya Yaba Wa Shugaba Tinubu kan Gyare-Gyaren Tattalin Arziki Da Samar da Tsaro

Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya yaba wa jagorancin  Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, inda ya bayyana cewa gyare-gyaren tattalin arzi...

Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya yaba wa jagorancin  Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, inda ya bayyana cewa gyare-gyaren tattalin arziki da tsare-tsaren tsaro da gwamnatin ke aiwatarwa sun kawo sakamako mai kyau da tasiri a fadin Jihar Bauchi da ƙasa baki ɗaya.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin da ya karɓi baƙuncin Ministan Kuɗi da Kula da Tattalin Arziki, Taiwo Oyedele, tare da Ministan kula da Kiwon Lafiya da Jin Daɗin Jama'a, Dr. Muhammad Ali Pate, waɗanda suka kai masa ziyarar ban-girma a Gidan Gwamnati da ke Bauchi.

Yayin da yake miƙa goyon bayan jihar, Gwamna Mohammed ya bayyana cewa manufofin Gwamnatin Tarayya na yanzu suna samar da cigaba a aikace.

 Ya tabbatar da cewa al'ummar Jihar Bauchi suna da masaniya kuma suna godiya ga ƙoƙarin gwamnatin wajen daidaita tattalin arziki da magance matsalolin tsaro, sannan ya yaba da kyakykyawar dangantakar da ke tsakanin gwamnatin tarayya da shugabannin jihohi.

Gwamnan Bauchin ya kuma jinjinawa shugaban ƙasa kan samar da ayyukan cigaba ba tare da la'akkari da bambancin siyasa ba inda ya bada misali da jihar sa ta Bauchi da kuma Oyo.

A ɓangaren samar da tsaro Gwamna Bala Mohammed ya jinjinawa yadda shugaban ƙasa ya aike da jami'an tsaro karkashin kulawar NSA da hukumomin soja wanda suka fatattaki ƴan bindiga da suka addabi jihar a baya.
 

No comments