Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya kaddamar da Titin Kuje wanda ya haɗe da babbar hanyar zuwa filin sauka da tashin jiragen sama a Abuja, ...
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya kaddamar da Titin Kuje wanda ya haɗe da babbar hanyar zuwa filin sauka da tashin jiragen sama a Abuja, inda ya ce gwamnatinsa ba ta yi watsi da ayyukan da ta gada ba, sai dai ƙara ƙarfafa su.
Mataimakin Shugaban ƙasa, Kashim Shettima, wanda ya wakilce shi, ya ce kammala titin mai layuka shida wata alama ce ta cika alkawuran Ajandar Sabuwar Fata ta gwamnati.
Tinubu ya bayyana cewa titin, wanda aka fara a 2022 aka watsar da shi, ya janyo cunkoso, ƙura da ambaliya, amma yanzu zai rage lokacin tafiya, tare da bunƙasa tattalin arziƙi da sauƙaƙa harkokin kasuwanci.
A nasa jawabin, Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ce aikin ya kasance mai wahala amma an kammala shi domin dawo da fata ga mazauna yankin.
Ita ma Ƙaramar Ministan Abuja, Dr. Mariya Mahmoud, ta ce aikin wata babbar nasara ce wajen inganta rayuwar al’umma a Abuja.







No comments